Shugabannin Iran da Isra’ila sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya a kan rikicin Syria
A yau ne rahotanni suka bayyana cewar an yi wata ganawar sirri a Amman, babban birnin kasar Jordan, tsakanin shugabannin kasar Isra’ila da na Iran a kan rikicin kasar Syria da ya ki-ci-ya-ki cinyewa.
Ana saka ran za a gwabza wani rikici a kudu maso yammacin kasar Syria kuma a kan hakan ne shugabannin suka gana tare da cimma yarjejeniyar cewar, dakarun Iran ba zasu shiga cikin rikicin ba.
Jaridar Ilaf ta kasar Saudiyya, mai cibiya a Landan, ta rawaito cewar, jakadan kasar Iran a Jordan, Amman Mujtaba Firdaus Bur da mataimakin rundunar tsaron kasar Iran na daga cikin wadanda suka samu dammar halartar taron da wani jagora a kasar Jordan ya shiga tsakani domin kulla yarjejeniyar.
Ana saka ran za a samu rikici a kudu maso-yammacin kasar Syria, musamman a garuruwan Dera da Al-kunaytra inda kuma yayin tattaunawar aka amince da cewar kungiyar ‘yan shi’a da suka hada da Hizbullah ba zasu shiga cikin gwabzawar da za a gwabza tsakanin sojoin Asad da ‘yan adawa a yankin ba.
DUBA WANNAN: Kasar Amurka ta dawo da wani dan Najeriya gida saboda latsa karamar yarinya
Kazalika kasar Ira’ila dake da iyaka da yankin ta tsaunukan Golan, ta bayyana cewar ba zata saka hannu cikin rikicin ba matukar kungiyoyin shi’a za su koma gefe.
Wasu rahotanni sun bayyana cewar an yi wannan taro da kulla yarjejeniya ne da masaniyar kasar Rasha.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng