Tompolo, Ateke Tom, tare da wasu shugabanni a Niger Delta sun nuna goyon baya ga gwamnatin tarayya

Tompolo, Ateke Tom, tare da wasu shugabanni a Niger Delta sun nuna goyon baya ga gwamnatin tarayya

- Manya-manyan shugabannin kungiyoyin Niger Delta, sun daura damarar taya gwamnantin tarayya kokarin kara tabbatar da zaman lafiya a yankunan dake da mai domin samun samun gudanar da zaben 2019 cikin kwanciyar hankali

- Shuwagabannin sun hada da Chief Bibopre Ajube, wanda akafi sani da General Shoot-at-Sight; Victor Ben, alias Boyloaf, da HRH Ateke Tom, sai kuma Ekpemupolo alias Tompolo

- Mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin al’amuran Niger Dalta, Mista Murphy Ganagana, ya bayyana cewa akwai al’amuran da suka kamata gwamnatin tarayya ta gyara domin tabbatar da zaman lafiya a yankunan

Manya-manyan shugabannin kungiyoyin Niger Delta, sun daura damarar taya gwamnantin tarayya kokarin kara tabbatar da zaman lafiya a yankunan dake da mai domin samun samun gudanar da zaben 2019 cikin kwanciyar hankali.

Shuwagabannin sun hada da Chief Bibopre Ajube, wanda akafi sani da General Shoot-at-Sight; Victor Ben, alias Boyloaf, da HRH Ateke Tom, sun bayyana goyon bayansu ga gwamnatin tarayya a karshen satin da ya gabata, a jihar Legas, lokacin da suka gudanar da taro da mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin al’amuran Niger Delta, Prof. Charles Dokubo.

Babban mataimakin mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin al’amuran Niger Dalta, Mr. Murphy Ganagana, ya bayyana cewa akwai al’amuran da suka kamata gwamnatin tarayya ta gyara domin tabbatar da zaman lafiya a yankunan.

Richard Akinaka, wanda ya wakilci Ateke Tom, yace mutanen jihar Rivers, musamman ‘yan kabilar Okrika, suna goyon bayan shirin bayar da kariya ga mutanen yankin wanda gwamnatin tarayyar ta shirya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng