Za a karawa Malaman Makaranta a Najeriya albashi – Ministan ilmi

Za a karawa Malaman Makaranta a Najeriya albashi – Ministan ilmi

- Gwamnatin Buhari na shirin kara albashin Malaman Makaranta a Najeriya

- Ministan ilmi na kasar dai ya bayyana wannan a Ranar Alhamis da ta wuce

- Hakan zai sa a ba harkar ilmi muhimmancin da ya dace a Kasar inji Minista

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kwanan nan albashin Malaman Makaranta zai dara na sauran Ma’aikata a Najeriya. Za ayi haka ne domin bunkasa tsarin ilmi a Kasar ya zama koyarwa ya zama aikin su wane-da-wane ba kowane shirbici ba.

Za a karawa Malaman Makaranta a Najeriya albashi – Ministan ilmi
Gwamnatin Najeriya za tayi koyi da Malaysia a harkar ilmi

Ana sa rai Malaman Makaranta za su fara karbar albashi mai tsoka ne a Najeriya a karkashin Gwamnatin Shugaba Buhari kamar yadda Ministan ilmi na Kasar ya bayyana lokacin kaddamar da Majalisar kwalejin ilmi na kasar a makon jiya.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bankado irin barnar da Obasanjo yayi

A Ranar Alhamis da ta wuce ne Mallam Adamu Adamu ta bakin Karamin Ministan ilmin kasar watau Farfesa Anthony Anwukah yayi wa Malaman Makarantan Kasar albishir da cewa za a kara albashin su kamar yadda ake yi a irin su Kasar Malaysia.

Sai dai kuma Ministan a lokacin da ya wakilci Mallam Adamu Adamu ya bayyana cewa Malaman Makarantar da ba su da rajista da Hukumar TRCN ta kasa za su gamu da babbar matsala domin kuwa za a kore su daga bakin aiki a karshen bana.

Farfesa Anthony Anwukah yake cewa a Malaysia wadanda su ka fi hazaka su na kokari ne na zama Malaman Makaranta domin kuwa nan ake biyan albashi mai tsoka. Anwuka yace sai ka samu masu Digirin PhD su na koyarwa a Firamare a can.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel