Wata mai wurin sayar da abinci da aka zarga da maita ta zunduma cikin teku

Wata mai wurin sayar da abinci da aka zarga da maita ta zunduma cikin teku

Wata mai tallar abinci ta kashe kan ta bayan an zarge ta da maita. Rahotanni sun bayyana cewar matar, mai shekaru 31, ta kasha kan ta ne a daren jiya, Asabar.

An ce ta tsunduma cikin tekun Naija da misalign karfe 9:00 na daren jiya bayan ta tsinewa mutanen dake zargin tad a maiata.

Jaridar Daily Post ta rawaito cewar matar, Stella Ndukwe, ta yanke shawarar kashe kan ta ne bayan zargin ta da ake yi da maita na kara yaduwa.

Wata mai wurin sayar da abinci da aka zarga da maita ta zunduma cikin teku
Wata mai wurin sayar da abinci da aka zarga da maita ta zunduma cikin teku

Majiyar Daily Post ta sanar da ita cewar, wani tsohon saurayin matar ne ya fara kwarmata zancen maitar Stella bayan ya samu labarin cewar tana fadawa mutane cewar sun rabu ne saboda bashi da karfin alkalami.

Majiyar ta kara da cewar an taba zargin Stella da maita a kauyen ta dake Adaeke Nuku dake jihar Anambra, dalilin da yasa ta bar garin tare da komawa Asaba, jihar Delta, inda ta fara sana’ar sayar da abinci.

DUBA WANNAN: An canja DPO din ofishin 'yan sanda dake cikin ginin majalisa

Stella ta shiga matsananciyar damuwa ne bayan jama’a sun kauracewa wurin cin abincin tad a a baya jama’a ke cika makil, hakan ya saka ta komawa sayar da abinci a wilbaro amma duk da haka jama’a basa son sayen abinci a wurin ta.

Wata kawar Stella ta ce, ta shaida mata cewar ta gaji da rayuwar duniya saboda komai nata lalacewa yake yi ga shi kowa na kiran ta maiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel