UCL: Yadda Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turan ta na 13 a Tarihi
A jiya ne dai aka buga wasan karshe na Zakarun Nahiyar Turai tsakanin Madrid da Liverpool. Real Madrid ta kafa tarihi a Duniya bayan doke Liverpool din da ci 3-1. Gareth Bale da Karim Benzema ne su ka zura kwallayen.
Wannan nasara da Real Madrid ta samu a Gasar Champions League na nufin Kulob din tayi nasarar daga kofin sau 3 a jere kuma wannan ne ya zama karo 4 da Real Madrid ta dauki Kofin na Nahiyar Turai daga 2014 zuwa yanzu.
Real Madrid ta fara lekawa ragar ne bayan an dawo hutun rabin lokaci bayan da mai tsaron ragar Liverpool Lorius Karius yayi wannan shirme kwallo ta fada kafar Karim Benzema. Bayan ‘Yan mintina kadan Sadio Mane ya rama.
KU KARANTA: Ban da niyyar auren mata 2 Inji Ronaldinho
Kafin nan dai dole ta sa Mohammed Salah ya bar filin bayan ya samu rauni sanadiyyar karo da yayi da Sergio Ramos. Bayan sako Gareth Bale kenan ya ci wata kwallo da ta shiga tarihi. Bayan wani lokaci kuma Bale din ya kara wata.
A tarihi dai ba a taba samun wanda yayi wannan kokari irin na Koci Zinedine Zidane ba wanda kafin nan ya ci kofin. Shi kuwa 'Dan wasan gaban Kungiyar Cristiano Ronaldo da ya fi kowa yawan kwallaye ya daga kofin karo na 5 a rayuwar sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng