Kowa ya bi: Tsaffin tsegerun Neja Delta sunci alwashin sai Buhari ya yi tazarce

Kowa ya bi: Tsaffin tsegerun Neja Delta sunci alwashin sai Buhari ya yi tazarce

- Tsohon shugaban tsagerun Neja Delta, Janar Lawson ya ce shugaba Buhari ya taka rawar gani sosai a shekaru uku da suka gabata saboda haka zai tabbatar da cewa shugaban ya zarce

- Lawson ya ce zai tattaro tsaffin kwamandojinsa don su tabbatar cewa ya samar wa shugaba Buhari kuri'in yankin

- Tsohon shugaban tsagerun ya ce a shirye ya ke ya yi yaki da takwarorinsa a yankin inda har za su taka masa birki a kan burinsa

Tsohon shugaba tsagerun Neja Delta na Phase II, wanda suka amfana da shirin Amnesty na shugaban kasa, 'Janar' Emma Lawson da lashi takobin tabbatar da cewa shugaba Buhari ya yi nasara a yankin a zaben 2019.

Lawson ya ci alwashin kare kuri'un shugaba Muhammadu Buhari a yankin Neja Delta mai albarkatun man fetir a zaben 2019 kamar yadda jardiar Vanguard ta ruwaito.

A yayin wata zantawa da manema labarai a Abuja cikin kwanakin nan, Lawson ya yi barazanar magance duk wani wanda ya yi yunkurin karkatar da kuri'un shugaba Buhari a yankin.

Kowa ya bi: Tsaffin tsegerun Neja Delta sunci alwashin sai Buhari ya yi tazarce
Kowa ya bi: Tsaffin tsegerun Neja Delta sunci alwashin sai Buhari ya yi tazarce

KU KARANTA: Wata rigimamiyar mata ta kaiwa alkali farmaki a kotu yayin da ake zaman shari'a

Tsohon tsageran ya yi imani cewa a cikin shekarun uku da ya yi, shugaba Muhammadu Buhari dara tsohon shugaban Goodluck Jonathan aiki duk da cewa shekaru shida ya kwashe. "Bisa la'akari da abubuwan da ke faruwa a siyasar yankin Neja Delta, Ni 'Janar' Emma Lawson, shugaban tsaffin tsagerun Neja Delta kuma kwamandan Neja Delta nayi alkawarin cewa zan samar wa shugaba Buhari kuri'u kuma in kare kuru'in a zaben 2019.

"Na kuma yi alkawarin jagorantan sauran tsaffin kwamandojin da ke karkashi na don taimakan min sauke wannan aikin ba tare da tsoro ko fargaba ba kuma duk wani tsohon tsagera ko matashi da ya yi yunkurin taka min birki zai fuskanci hukunci irin wadda da dace da dokar kasar mu."

Ya ce wannan sanarwan da ya yi shaida ce da ke nuna ya amince da jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da nasarorin da ya samu a yankin Neja Delta cikin shekaru uku na mulkinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164