Wata mace ta kwancewa mijinta zani a kotu, ta kuma bukaci a raba aurensu

Wata mace ta kwancewa mijinta zani a kotu, ta kuma bukaci a raba aurensu

Wata mace mai shekaru 35 a duniya, Remilekun Familusi ta roki wata kotu da ke zamanta a Abeokuta ta katse igiyar aurenta da mijinta Olayinka saboda halin kuruciyar bera da ta gano yana dashi.

Matar ta shaidawa kotu cewa Allah ya basu diya guda a zaman auren da sukayi na shekaru biyar.

Remilekun tayi ikirarin cewa mijinta barawo ne kuma dan damfara ne wanda sau da yawa mutanen da ya damfara ko ya yiwa sata sukan zo nemansa ruwa a jallo a gida.

Ta ce tun dama tun da fari, mijin nata ba mutumin kirki bane. Yakan sato abincin jarirai da kayayakin masarufi daga shaguna ya kawo mata gida don ta ciyar da jaririyarsu.

Wata mace ta kwancewa mijinta zani a kotu, ta kuma bukaci a raba aurensu
Wata mace ta kwancewa mijinta zani a kotu, ta kuma bukaci a raba aurensu

KU KARANTA: An damke sojoji da tsaffin 'yan sandan cikin gungun wasu 'yan fashi da makami

"Na dena karban kayayakin abinci da ya ke kowo wa gida bayan da na gano cewa satowa ya keyi daga shaguna.

"Bamu taba wata zama na soyaya ba a matsayin ma'aurata, baya taba nuna wasu halayen dattaku.

"Bayan na haifi diya ta a shekarar 2013, na baro gidan iyayensa inda na ke zaune," inji Remilekun.

Ta kara da cewa akwai lokuta da dama da mahaifinta ke belinsa daga caji ofis bayan an kama shi saboda sata. Da hakan ne ta roki kotu ta raba aurensu kuma ta roki kotu ta bar mata rainon yarsu guda daya.

Ta kuma bukaci kotu ta hana Olayinka ziyartar gidanta ko kuma makarantar diyarsu saboda fitina ya ke zuwa ya haddasa.

A bangarensa, Olayinka ya shaidawa kotu cewa dama tun farko ba kaunarta ya keyi ba, ya ce idan ba dalilin diyarsu ba da tuni ya nemi a raba auren.

Ya kuma yi ikirarin cewa yana kulawa da ita da diyarsu inda ya nuna wa kotu takardun banki na kudaden da ya ke tura mata da kuma wadanda ya tura ta asusun bankin surukarsa.

Olayinka ya kuma shaidawa kotu cewa ya dena sata da damfara, ya kuma kara da cewa Allah ya kawo masa canji a rayuwarsa.

Olayinka ya amince kotu ta raba auren sai dai shima ya bukaci a mallaka masa rainon diyarsu wanda ya kwashe watanni 18 bai ganta ba.

Alkalin kotun, Olalekan Akande ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Yuni inda ya ke sa ran ayi sulhu ko kuma ya zartar da hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164