Buhari ya nada shugaban ‘yan sanda da Obasanjo ya kora a wani babban mukami

Buhari ya nada shugaban ‘yan sanda da Obasanjo ya kora a wani babban mukami

A yau ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nada tsohon shugaban rundunar ‘yan sanda, Musliu Smith, a matsayin sabon sabon shugaban hukumar ‘yan sanda (PSC).

Shugaban majalisar dattijai, Bukjola Saraki, ya karanta wasikar neman amincewa da Smith da wasu mutane uku da shugaba Buhari ya aikowa majalisar.

A ranar 29 ga watan Mayu, 1999, Obasanjo ya nada Mista Smith a matsayin shugaban rundunar ‘yan sanda na kasa (IGP) kafin daga baya yak ore shi a ranar 1 ga watan Fabrairu na shekarar 2002, bayan jami’an ‘yan sanda sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya. Yajin aikin jami’an ‘yan sandan ya matukar fusata Obasanjo tare da bashi mamaki, lamarin day a saka shi cire Smith daga kan kujerar sa.

Buhari ya nada shugaban ‘yan sanda da Obasanjo ya kora a wani babban mukami
Buhari ya nada shugaban ‘yan sanda da Obasanjo ya kora a wani babban mukami

Jami’an ‘yan sandan sun shiga yajin aikin ne, a wancan lokacin saboda rashin yarda da shugabancin Smith bayan ya yi wani yunkuri na kawo karshen matsalar matsuguni da jami’an ‘yan sanda ke fuskanta.

DUBA WANNAN: An tarwatsa magoya bayan Shekarau da barkonon tsohuwa a kotun da aka gurfanar da shi

Gwamnatin Obasanjo ta amince zata biya jami’an ‘yan sanda da basu samu muhalli a barikin ‘yan sanda ba kudin haya, amma sai daga baya ta janye wannan alkawari, lamarin da ya saka jami’an ‘yan sandan tafiya yajin aiki bisa zargin cewar Mista Smith ne ya cinye kudin su.

Ana rade-radin cewar Tinubu da Fashola na da hannu cikin nadin Mista Smith, musamman ganin cewar gwamnatin jihar Legas ce, lokacin da Tinubu ke gwamna, ta fara bashi mukami kafin daga bisani Fashola ya nada shi a matsayin shugaban hukumar tsaron jihar a shekarar 2007.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel