Kamfanoni 27 da suka yi watanda da kudin kwangilar aikin wutar lantarki a zamanin Obasanjo

Kamfanoni 27 da suka yi watanda da kudin kwangilar aikin wutar lantarki a zamanin Obasanjo

Biyo bayan tayar da kura da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi game da yadda gwamnatin Obasanjo ta yi ikirarin kashe dala biliyan 16 a harkar wutar lantarki da kuma martanin da Obasanjo ya mayar ma Buhari, jaridar The Nation ta gudanar da zuzzurfan bincike.

Majiyar Legit.ng ta ci karo da wani rahoto da hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta fitar bayan wani binciken kwakwaf da ta gudanar akan lamarin, inda tace gwamnatin Obasanjo ta kashe triliyan 1.2 a harkar wuta, amma naira biliyan 360.7 ne kadai ya isa hannun yan kwangila, ya rage saura N870, 234, 918, 828.06.

KU KARANTA: Yansandan Najeriya sun yi caraf da wasu gagga gaggan masu garkuwa da mutane su 14

EFCC ta ce gwamnatin Obasanjo ta sake kashe kudi naira biliyan 273.65 a kamfanin wutar lantarki na Najeriya, PHCN, tun daga shekarar 1999 zuwa 2007, haka zalika kamfanin ta karbi kudaden kwangilolin daban daba; N22.297billion and 162,467.57billion; dala 445.244.630.07; Yuro 20, 105,436.31; da pan 8,987,322 na wutar lantarki da aka baiwa kamfanoni 27.

Kamfanoni 27 da suka yi watanda da kudin kwangilar aikin wutar lantarki a zamanin Obasanjo
tashar wuta

Ga dai Jerin kamfanoni 27 da hukumar EFCC a karkashin tsohon shugabanta Ibrahim Lamurde suka gano sun amfana da kwangilar, da kuma kudin da aka bada kwangilolin akai:

Pivot Engineering Ltd dala miliyan 78

ABB {Nig] Ltd [SAE] dala miliyan 21 da naira biliyan 489,271,079.60

Siemens Ltd Yuro miliyan l5, 032,410.65 da naira miliyan 200

Energovod Src dala miliyan 42 da naira miliyan 900

AREYVA T/D SPR-and -MBH power pan miliyan 8.9 da naira miliyan 600

Chrome Consortium dala miliyan 74.8

News Engineering dala miliyan 3.4 da naira miliyan 250

Pivot Engineering dala miliyan 4

Valenz Holdings [Nig] Ltd dala miliyan 7 da naira miliyan 489

Kec/News Engineering dala miliyan 30 da naira biliyan 2.5

JKN Limited N822 million

LCEP dala miliyan 50

ABB dala miliyan 12.5 da Yuro miliyan 1.7

Energo (Nig) Limited dala miliyan 8.4 da naira miliyan N141.9

SAE Power Lines and Areva (SIS) naira biliyan l.2

News Engineering Nig Limited naira miliyan 441.5 da naira miliyan 251.7

Continental Engineering Nig Limited naira miliyan 453

News Engineering Limited dala miliyan 1.2

ABB Power Katempe naira miliyan 347

ABB Nigeria Limited Yuro miliyan 2.8 da naira miliyan 109.9

Valenz Holdings Nigeria Ltd Yuro miliyan 4.4 da naira miliya 251.9

CMC dala miliyan 30

Steers Int’l Ltd dala miliyan 1.4 da naira miliyan l52

SEPCO dala miliyan 30

NCEP dala miliyan 5.2 da naira miliyan 272

CCC Int’l Ltd dala miliyan 2.6 da naira miliyan 198.

Sai dai wannan rahoton da ya fito daga hukumar EFCC bai gano wata alaka ko dantanka a tsakanin dukkanin kamfoninnan guda 27 da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba, ko kuma wani dan uwansa na jini, ko abokai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng