Boko Haran sun fi shekaru 25 a Najeriya – Inji Janar Buba Marwa

Boko Haran sun fi shekaru 25 a Najeriya – Inji Janar Buba Marwa

Kwanaki mu ka ji labari daga Daily Trust cewa Tsohon Gwamnan Jihohin kasar nan a lokacin a lokacin mulkin Soja Birgediya Janar Buba Marwa yace akwai Yan ta’addan Boko Haram sama da shekaru 20 da su ka wuce a Najeriya.

Boko Haran sun fi shekaru 25 a Najeriya – Inji Janar Buba Marwa
Buba Marwa yayi Gwamna a Jihar Borno a 1992

Tsohon Gwamnan na Jihar Legas da Borno a lokacin Soji Buba Marwa (Rtd) yace ‘Yan ta’addan da su ka rikida su ka zama ‘Yan Boko Haram a Yankin Arewa-maso-Gabashin Najeriya sun kai kimanin shekaru 25 a cikin Kasar nan.

KU KARANTA: Tsageran Neja-Delta yace ko za a mutu sai sun ga Buhari yayi nasara a zaben 2019

Janar Buba Marwa ya bayyana wannan ne a lokacin da yake jawabi wajen wani laccar musamman kan Watan Azumin Ramadan da Kungiyar Musulunci ta “Al-Habibiyyah Islamic Society” ta shirya a wancan makon a Birnin Tarayyan Abuja.

Marwa yace tun a lokacin da yake Gwamnan Jihar Borno akwai shigen ‘Yan ta’addan wanda daga baya burbushin su ne su ka zama Boko Haram. Marwa yace wadanda su kayi Gwamna a Jihar Borno bayan sa duk sun san wannan maganar.

Babban Janar din yace yayi kokari a lokacin sa 'Yan ta’addan lokacin su na da wani suna ba su dauki makamai su yi fada ba kuma ya nemi a marawa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari baya wajen yakin da ta ke yi da ‘Yan ta’addan a Kasar.

A dai wajen laccar irin su Farfesa Salisu Shehu sun yi kira ga Musulmai su taimakwa juna a lokacin wannan wata na Ramadan musamman yadda bincike ya nuna cewa Musulman Najeriya su na cikin wadanda fi kowa talauci a kaf fadin Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel