Abu 6 da masu azumi suka fi yawaita tambaya

Abu 6 da masu azumi suka fi yawaita tambaya

A yayin da Musulmi a duniya ke cigaba da azumtar watan Ramadana da muke ciki, wani malamin addini Islama kuma mahaddacin Alqur’ani, Shabbir Hassan, ya kawo jerin mas’aloli guda 6 da masu azumi suka fi yawaita tambaya a kan su tun farkon Musulunci.

Ga jerin abubuwan 6 kamar yadda Shehun Malami Shabbir ya zayyana su;

1. Yin aswaki ko goge baki da burushi yana karya azumi?: Wannan tambaya c eta da dade sosai ana yin ta kuma har yanzu ana cigaba da yin ta saboda mabanbantan fatawowi da ake samu daga wurin malamai.

Mafi rinjayen malamai sun fi karkata kan cewar babu laifi mai azumi ya goge bakin sa, saidai sun bukaci a yi taka-tsan-tsan wajen amfani da mana goge baki.

Abu 6 da masu azumi suka fi yawaita tambaya
Abu 6 da masu azumi suka fi yawaita tambaya

2. Ko mutum zai iya hadiye yawunsa?: Malamai a nan sun samu haduwa a kan fahimtar cewar babu laifi mutum ya hadiye yawun sa yayin azumi.

3. Ci da sha kawai aka hana da azumi?: Tabbas ba ci da sha kadai ke karya azumi ba, akwai ragowar abubuwa da sahari’a ta lissafa dake karya azumi.

4. Ko mutum zai iya shan magani ko a yi masa allura?: Wata majalisar malaman addinin musulunci ta ta Birtaniya (MCB) t ace masu lalurar ciwon ido da kunne kan iya cigaba da amfani da magungunan su koda kuwa da azumi a bakin su kuma ba tare da shan maganin ko allura ta karya shi ba.

DUBA WANNAN: Yadda mahaifina ya shafe tsawon shekara 4 yana lalata da ni - wata matashiya

5. Wajibi ne mutum sai yayi azumi duk halin da yake ciki?: Azumi ya wajaba ne a kan baligi mai lafiya. Bai wajaba a kan kananan yara da marasa lafiya ba dxa kuma jerin wasu mutane da shari’a ta lissafa.

6. Ci ko sha bisa mantuwa na karya azumi?: Matukar mai azumi bai cigaba da ci ko shan abun dake hannun sa ba bayan ya tuna, ci ko sha bisa kuskure ko mantuwa basa karya azumi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng