Duba kaga biliyoyin kudin da ma'aikatar man fetur ta tarawa Najeriya a cikin wata 6
Ma'aikatun Man Fetur na Najeriya, sun samar wa da Najeriya kudin shiga kimanin naira biliyan 13 a farkon shekarar nan ta 2018, hakan ya biyo bayan rahoton da hukumar hasashe ta kasa ta fitar wato National Bureau of Statistics (NBS) a turance
Ma'aikatun Man Fetur na Najeriya, sun samar wa da Najeriya kudin shiga kimanin naira biliyan 13 a farkon shekarar nan ta 2018, hakan ya biyo bayan rahoton da hukumar hasashe ta kasa ta fitar wato National Bureau of Statistics (NBS) a turance. Hukumar tace a rahoton da aka bayar na farkon wannan shekarar ya nuna cewar, ma'aikatun Mai dana Iskar Gas sun kawo wa Najeriya kimanin miliyan 8; inda kamfanonin sayar da man fetur suka samar da kimanin biliyan 2.512; matatun man fetur kuma suka samar da sama da biliyan 7; sai kuma matatun iskar gas wadanda suka samar da kimanin biliyan 1 da rabi.
DUBA WANNAN: Adadin mutanen da suka mutu a Najeriya cikin wata 6 sanadiyyar hadarin mota
A mafi girman matakin da aka rarraba bayanan, sun nuna cewar a farkon shekarar 2018 an samu kimanin naira biliyan 269.79, inda aka samu fiye da wanda aka samu a shekarar 2017, a shekarar 2017 dai rahoton ya nuna cewar an samu biliyan 254.10 a karshen shekarar, inda aka samu naira biliyan 221.38 a farkon shekarar 2017 din.
Hakan ya samar da kashi 6.17 cikin 100 a cikin kashi uku na shekara, inda ya samar da kashi 21.87 a shekara baki daya.
Da yake jawabi game da cigaban da aka samu a ma'aikatun man fetur din, Babban Daraktan Kamfanin NNPC na Najeriya, Dokta Maikanti Kachalla Baru, ya lura cewar Najeriya ta dauki kwakkwaran mataki akan kawo cigaba wurin harkar iskar Gas, domin ciyar da kasar gaba a kowanne fanni.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng