Kwakwazon da ake yi kan kashe-kashe a kasar nan yafi kashe-kashen yawa - El-Rufai
- Ana ta kashe mutane a jihar Kaduna
- Ana kuma kashe-kashe a sauran sassan kasar nan
- Gwamnan ya koka kan zuzuta wa da jaridu keyi
A hirarsa da BBC Hausa a dazu da safe, gwamnan jihar Kaduna, kuma mukarrabin Shugaba Buhari na APC, yace 'yan jarida da masu yada labarun soshiyal midiya na dandalin sada zumunta, su suke zuzuta kisan da ake yi a sassan Najeriya.
A cewar gwamnan, kisan dai mummunan abu ne, amma yadda ake yayata kisan in ya faru, sai ka dauka duk kasar ce ta kama da wuta.
A Girnin Gwari da sauran kudancin jihar dai ta Kaduna, ana samun kisan kai kone kauyuka da ma sace mutane, wanda ke da alaka da kabilanci da ma fashi da makami da garkuwa da mutane.
Akwai ma rikicin makiyaya da fulani Bororoji masu yawon kisa kan shanunsu da aka sace ko aka kashe musu masu kiwo.
DUBA WANNAN: Sabbin nade-naden da shugaba Buhari yayi a yau
Ya zuwa yanzu dai, babu alamar kashe-kashen zasu zo karshe, duk da cewa shekara guda cif-cif ta rage wa gwamantin da tayi alkawarin dawo da tsaro a fadin kasar nan. Suma kuma a baya lokacin basu gwamnati, 'yan APC, basu yi ma gwamnatin PDP uzuri ko saukaka yada labarin kashe-kashen ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng