Ran mijina ya dawo bayan na nacewa Allah da azumi da ibada - Wata matar aure
- Wata mace yar kasar Tanzania ta yi ikirarin cewa mijinta ya rasu a watan Mayun 2018
- A cewarta, ba tayi jimamin rashinsa sosai ba saboda zuciyarta na raya mata cewa mijin na bai gushe ba
- Ta ce wai ta tsundunma cikin addu'o'i da yin azumi tare da wasu limaman coci har sai da ran mijinta ya dawo jikinsa
Wata mace yan asalin kasar Tanzania ta bawa mutane mamaki a yayinda ta yi ikirarin cewa mijinta da ya rasu watanni biyu da suka gabata da dawo da ransa bayan ta dage da yin addu'o'i da azumi.
Matar ta ce sunan mijinta Richard David Tarimo kuma ya mutu a ranar 30 ga watan Mayun 2018. Ta ce mijinta ya tashi daga matatu a ranar Litinin 21 ga watan Mayu bayan ta dage da yin addu'o'i da azumi tare da wasu limaman coci.
A wata hira da akayi da ita ranar 22 da ga watan Mayu, matar yar asalin garin Rombo da ke yankin Kilimanjaro ta ce Tarimo ya kamu da ciwon rashin iya numfashi a ranar Alhamis 29 ga watan Maris kuma ya rasu a hanyar mu na kai shi asibiti.
KU KARANTA: Wani saurayi ya kashe budurwar sa, ya cusa gawar ta cikin kwandon shara
"Mijina ya kamu da ciwon zuciya, mun kama hanyar tafiya dashi asibiti amma sai ya ce ga garinku tun kafin mu karasa asibitin. Hakan yasa muka ajiye gawarsa a dakin ajiye gawa na asibiti kuma muka birne shi bayan kwana daya," inji ta.
Sai dai bayan kwanaki bakwai, matar ta ce ta lura cewa kasar da aka tara a samar kabarinsa ya baje bayan birne shi a ranar 5 ga watan Afrilu, hakan yasa ta kyautata tsamanin cewa ya fice daga kabarin.
Ta cigaba da cewa:"Na fara addu'o'i da azumi tare da fastocin cocin mu kuma daga baya na samu na samu wahiyi cewa mijina ya fice daga kabarinsa."
Ta ce bayan fara addu'o'in da azumin, ta fara ganin mijin na ta a yayinda ta ke gudanar da ayyukan ta na yau da kullum sai dai ba suyi magana ba saboda yana bacewa cikin lokacin kankani.
A cewarta, ta kara imani da abinda ta ke gani saboda wasu makwabtan ta sun fada mata cewa suna haduwa da mijinta a wuraren shakatawa har ma da wurin shan giya.
"Na cigaba da addu'a da azumi kuma jiya sai daya daga cikin fastocin ya taho da miji na gida duk da cewa akwai alamar gajiya sosai a tare dashi kuma ba muyi magana ba. Na yi imanin cewa akwai asiri da tsafi amma wannan dai aikin Ubangiji ne," inji ta.
Wani surukinta ya sake jadada wa gidan talabijin na Ayo labarinta inda ya ce surukinsa ya farfado bayan ya mutu sai dai yana sanya da wasu tufafi ne daban da wanda ake birne shi da su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng