Go TV Cup: An tashi 3-2 tsakanin Kungiyar Atletico Madrid da Najeriya

Go TV Cup: An tashi 3-2 tsakanin Kungiyar Atletico Madrid da Najeriya

- Kungiyar Atletico Madrid ta zo har gida ta doke Super Eagles

- An tashi wasan da aka buga a Jihar Akwa-Ibom ne da ci 3-2

- Torres ya jefa kwallo a wasan karshen sa a Kulob din na sa

Zakarun Kofin Europa na Nahiyar Turai na bana watau Kungiyar Atletico Madrid na Kasar Sifen sun doke Kungiyar Super Eagles na Najeriya sun dauki kofin Go TV a wani wasa da aka buka na kawance a jiya da yamma.

An tashi 3-2 tsakanin Kungiyar Atletico Madrid da Najeriya
'Dan wasan Atletico Madrid Torres ya ci Najeriya a wasan sa na karshe Hoto daga: BBC Hausa

Atletico Madrid ta zo har Garin Uyo ne a Jihar Akwa-Ibom ta doke Najeriya da ci 3-2. Najeriya ce dai a fara zuba kwallo a minti na 31 ta hannun Kelechi Nwakali. ‘Dan wasa Angel Correa ne ya ramawa Atletico ya kai wasan 1-1.

KU KARANTA: Wani rasuwa da aka yi ya girgiza Jihar Gombe

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne dai aka sa ‘Dan wasa Fernando Torres inda ya kuma ci bayan ya shigo. Wannan ne wasan sa na karshe da Kungiyar ta Atletico Madrid. Torres ya bugawa Chelsea da Liverpool a rayuwar sa.

Usman Mohammed ya ci kwallo mai kyau bayan ya yanke ‘yan bayan Atletico a kusan Minti na 80. Sai dai Borja Garces ya zurawa Najeriya kwallo a raga a karshen wasan inda aka tashi 3-2. Nan gaba Najeriya za ta kara da Congo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel