Wai! Wani Maigida ya tsallake rijiya da baya yayin da matarsa ta girka masa Abincin bera

Wai! Wani Maigida ya tsallake rijiya da baya yayin da matarsa ta girka masa Abincin bera

Wata Kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a Unguwar Magajin Gari na jihar Kaduna ta kawo karshen aure tsakanin wasu ma’aurata Surajo Abdullahi da Nazirra Ahmad, bisa matsaloli da dama da suka taso a tsakaninsu, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Uwargida Nazira ce ta kai karar mijinta gaban Kotu a ranar 2 ga watan Mayu, inda ta zargi mijin da cin zarafinta, cin mutuncinta tare da gaza nauyinta da ya rataya a wuyansa.

KU KARANTA:Karfin shari’a: Wani Mutumi ya yi barazanar kashe makwabcinsa, ya ɗanɗana kuɗarsa

Sai dai Surajo ya musanta zarge zargen matartasa, inda yace shi ma ya kamata ya koka da ita, tunda ta taba sanya masa maganin bera a cikin abincinsa, wanda da kyar ya sha, sa’annan tana neman maza.

Wai! Wani Maigida ya tsallake rijiya da baya yayin da matarsa ta girka masa Abincin bera
Kotun Musulunci

A zaman sauraron karar na farko da aka yi a ranar 2 ga watan Mayu, Alkalin ya umarci waliyyi Amarya da wakilin Maigida da su gurfana a gabansa a ranar Talata 22 ga watan Mayu, inda bayan sauraron bayanan su, Alkali Dahiru Lawal ya fahimci ma’auratan basu bukatar cigaba da zama.

Wakilin Ango, Lawal Usman ya bayyana ma kotun cewa sun sha shiga tsakanin ma’auratan kan matsaloli da dama da ya faru, amma basu samu maslaha ba, don haka yace tun da dai abin ya kai ga sanya guba a cikin abinci, gwara a raba auren kawai kowa ya huta. Hakanan shi ma waliyyin Nazira, Usman Ahmad ya bayyana ma Kotu gamsuwa da raba auren.

Daga nan bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu sai Alkali Dahiru ya raba auren, “Tunda dai aure ba wai batun a mutu ko ayi rai bane.” Inji shi.

“Tun da dai matarka bata kaunar cigaba da zama tare da kai, kuma kai ma ma tabbatar da cewa ta sanya maka guba abinci, kuma iyayenku sun amince da kashe aurenku, don haka ni Dahiru Lawal, Alkalin Kotun shari’ar musulunci dake Magajin gari, jihar Kaduna na raba aure tsakanin Suraju Abdullahi da Nazira Ahmad, kun tashi daga matsayin mata da miji.” Inji Alkali.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel