Buhari ya kalubalanci Obasanjo a kan kashe $16bn a fanin wutan lantarki
Shugaba Muhammadu Buhari ya saka alamar tambaya a kan yadda gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanja ta kashe $16 biliyan a kan aikin samar da wutan lantarki a Najeriya.
Shugaba Buhari ya yi tsokaci a kan lamarin ne a yayin da ya ke jawabi a fadar Aso Villa a lokacin da ya ke tarbar tawagar kungiyar magoya bayan sa karkashin jagorancin shugaban hukumar hana fasakwabri (kwastam), Ahmed Ali.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Bayan ya zame hanunsa daga sharia'r a jiya, lauyan Olisa Metuh ya dawo kotu
Duk da cewa shugaba Buhari bai ambaci sunan Obasanjo ba, amma ya ce "ina wutan lantarkin da aka samar alhalin wani tsohon shugaban kasa ya yi ikirarin kashe $16 biliyan wajen aikin gyaran wutan."
A shekarar 2008, majalisar wakilai ta bayyana cewa $16 biliyan da gwamnatin Obasanjo ta kashe wajen ayyukan samar da wutan lantarki a matsayin babban asarar kuma ta ce rashin tsara kasafin kudi mai kyau da sa ido a kan aikin ne ya janyo hakan.
Wata kungiya mai fafutukan tabbatar adalci da kwato wa yan Najeriya hakkinsu a shekarar 2016 ta bukaci Alkalin alkalai na wucin gadi, Justice Walter Samuel Onnoghen ya kafa wata kwamitin bincike mai zaman kanta don bincike a kan $16 biliyan da gwamnatin Obasanjo ta kashe a fanin wutan lantarki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng