Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kasha jami’in DSS 1, sun sace biyu

Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kasha jami’in DSS 1, sun sace biyu

Wasu tsagerun ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai wani farmaki jihar Benuwe tare da kasha wani jami’in tsaro na hukumar DSS tare da sace wasu biyu kamar yadda wasu majiya suka tabbatar wa da jaridar Premium Times afkuwar lamarin.

A kalla soja guda ne ya rasa ran sa tare das ace wani sojan yayin harin da ‘yan bindigar suka kai karamar hukumar Logo mai fama da yawan hare-hare. Lamarin ya faru nme ranar Lahadi.

Mun tabbatar da kashe wani jami’in DSS guda daya tare da sace wasu biyu,” wata majiya a cikin jami’;an tsaro ta tabbatar wa jaridar Premium Times.

Tuni hukumar soji ta tabbatar da kashe mata jami’i guda tare das ace wani, saidai hukumar DSS har yanzu bata fitar da sanarwa dangane da faruwar lamarin.

Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kasha jami’in DSS 1, sun sace biyu
Anyi musayar wuta da asarar rayuka tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindiga

An cakuda jami’an DSS cikin rundunar soji ne domin yaki da aiyukan ta’addanci tsakanin makiyaya da manoma dake cigaba da tayar da hankula a jihar Benuwe.

Harin ‘yan bindigar na ranar Lahadi na daga cikin hari mafi muni da aka kai kan jami’an tsaro tun bayan fara rikici a jihar Benuwe.

DUBA WANNAN: Jami'an tsaro sun nade wani shu'umin likita da ya kware a wani sabon salon damfara

Ko a kwanakin baya saida aka kasha jami’an ‘yan sanda 10 a wani hari da ‘yan bindiga suka kai masu da almuru.

Wani rahoto da hukumar soji ta fitar ya bayyana cewar a kalla makiyaya 35 daga cikin wadanda suka kawo harin sun mutu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel