Kamfanin jirgin Amurka ya gana da Ministan sufuri Amaechi domin aikin jirgin kasa na Dala Biliyan 10
Mun samu labari jiya cewa wani babban Kamfanin da ke harkar gine-gine a Kasar Amurka na neman kashe makudan kudin da su ka haura Dala Biliyan 10 domin gina titin-dogo na jirgin kasa a Najeriya kuma da dai alamu za a dace.
A Ranar Litinin dinnan labari ya zo mana cewa Kamfanin Ameri Metro Incorporation ta fadawa Gwamnatin Shugaba Buhari cewa za ta gina titin jirgin kasa na zamani a Najeriya ganin cewa Kasar China ta gaza cika alkawarin ta.
Kamfanin na Amurka yayi wa Ministan sufuri na Kasar watau Rotimi Amaechi bayanin yadda za su yi wannan aiki a Najeriya. A baya dai an shirya da wani Kamfanin Kasar China cewa za su yi wannan aiki amma abin sam bai yiwu ba.
KU KARANTA: An kama wata mata da zinari a tashar jirgin sama
Shugaban Kamfanin Shah Mathias yace a shirye su ke da su rangadawa Najeriya aikin jirgin kasa na zamani mai ‘dan-karen gudu da kudin su. Kamfanin tace ita za ta kashe duk kudin da ake bukata wajen wannan aiki wanda ya kai Biliyan $10.
Za a sa sabon titin dogo ne daga Fatakwal zuwa Legas har Garin Kalaba sannan kuma za a kawo sababbin jiragen kasa. Abin da ya hana ayi aikin a lokacin baya dai kurum shi ne rashin kudi daga Kamfanin da aka ba aikin na Kasar China.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng