Wani matashi ya zubar da hakoran maigidan sa da guduma a kan albashin wata 5

Wani matashi ya zubar da hakoran maigidan sa da guduma a kan albashin wata 5

Wani matshi, Isma’il Yusuf, mai shekaru 23 ya kaiwa wani maigidan sa Ba Indiye hari da guduma tare da zubar masa da hakora a kan rashin biyan sa albashin watanni biyar.

Matashin ya amsa cewar ya zubar da hakora 7 daga bakin Sattish Kasara, dan asalin kasar Indiya kuma manajan wani kamfanin haka rijiyoyi, Bolaji Drilling Company dake Minna a jihar Neja.

Lamarin da ya faru a yankin Tunga dake Minna ya yi sanadiyyar kama Yusuf.

Rahotanni sun bayyana cewar Kasara ya ki biyan Yusuf albashin sa ne saboda ya bayyana cewar yana son yin tafiya ya zuwa jihar Bauchi domin ganin iyayen sa.

Wani matashi ya zubar da hakoran maigidan sa da guduma a kan albashin wata 5
Matashi Yusuf

Yusuf ya shaidawa manema labarai cewar, ya roki ubangidan nasa day a taimaka ya biya shi hakkokin sa domin yana son tafiya gida domin ganin iyayen sa tare da alkawarin dawowa bayan sati guda amma ko sauraron sa Kasara bai yi balle ya bashi kudin da yake bukata. Bayan faruwar hakan ne Yusuf ya koma ofishin maigidan sa inda ya shiga a fusace ya buga masa guduma hart a kai gay a zubar masa hakora 7.

DUBA WANNAN: Gobara ta kona dakuna 12 da shago 1 a birnin Kano

Matashin ya kara da cewa, ya yiwa Kasara aiki na tsawon shekaru biyar ba tare day a taba ziyartar gida domin ganin iyaye da ‘yan uwan sa ba duk da irin cin mutuncin day a ce yana fuskanta a wurin bakin haure a kamfanin.

Kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar Neja, Muhammad Abubakar, y ace sun kwace gudumar Yusuf tare da wani bututu, kuma zasu gurfanar das hi gaban kotu da zarar sun kamala bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng