Kalli me aka ciro daga cikin wannan matar a Iyapot na jirgin sama

Kalli me aka ciro daga cikin wannan matar a Iyapot na jirgin sama

- An kama matar 'yar shekaru 25 a film hawa da saukar jirage dake babban birnin Delhi a ranar 14 ga watan Mayu

- 'Yan sandan sunce ta kwashe satin da ya gabata ne a asibiti inda aka ba magunguna don fitar da hodar iblis

Kalli me aka ciro daga cikin wannan matar a Iyapot na jirgin sama
Kalli me aka ciro daga cikin wannan matar a Iyapot na jirgin sama

'Yan sandan kasar India sunce sunyi nasarar cire sunqin hodar iblis guda 106 daga wata mata da ake zargin ta da kokarin shiga kasar da mugayen kwayoyi.

An kama matar 'yar shekaru 25 a filin hawa da saukar jirage dake babban birnin Delhi a ranar 14 ga watan Mayu.

'Yan sandan sunce ta kwashe satin da ya gabata ne a asibiti inda aka ba magunguna don fitar da hodar iblis din.

Miyagun kwayoyin an kintata cewa zasu kai na rupees miliyan 50 kwatankwacin Naira 130m kenan a kudinmu.

'Yar kasar Sri Lanka, an kamata da kusan kilogram 1 na zinari a cikin ta. 'yan sanda sunce matar ta hadiyi sunqin ne a Sau Paulo, kasar Brazil, kuma an bata umarnin kaisu ga wani Dan kasar Najeriya da ke Delhi, inji rahoton BBC.

DUBA WANNAN: PDP zata iya hadewa da tsofin abokai

Jami'ai daga bangaren masana Miyagun kwayoyi sun sanar da jaridar Hindustan Times cewa "wannan shine mafi yawan sunqin hodar iblis da suka taba fitarwa daga jikin mutum"

'Yan sandan dai yanzu sun bazama neman Dan kasar Najeriya wanda matar zata kaiwa Miyagun kwayoyin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng