Kifayen ruwa sun yi watanda da baƙaƙen fata masu zuwa ci rani ƙasar Italiya
Akalla mutane 31 da daya ne suka mutu a sakamakon kifawa da jirgin ruwa daya taso daga kasar Libya zuwa Italiya yayi, wanda ya cika makil da bakaken fata yan Afirka, masu zuwa ci rani.
Daily Mail ta ruwaito, daga cikin wadanda suka mutu akwai mata 18, da kananan yara uku, sauran kuma maza ne, tare da mutum 40 da suka bace sama ko kasa.
KU KARANTA: Kowa ya tuba don wuya, ba lada: Kamfanin Atiku, INTELS, ta nemi afuwan gwamnatin tarayya
Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa zuwa yanzu Sojojin ruwan kasar Libya sun ceto mutane 200 daga hatsarin, sai dai Sojojin sun tabbatar da ganin manyan kifayen ruwa zagaya jirgin bayan kifawarsa.
“A lokacin da muka iso wajen, mun tarar da wani jirgun ruwa ya kifa, har ya fara nutsewa, amma mun ceto da dama daga hatsarin. Mun tarar da gawawwaki da dama, haka zalika mun ga manyan kifayen ruwa suna kai kawo a gefen jirgin” Inji Nasser Al-Ghammoudi.
Daga cikin wadanda ake ceto, akwai yan Najeriya, Ghana, Etopiya da wasu yan Pakistan. Majiyar ta ruwaito cewar sakamakon kyawun yanayi da rashin ambaliyar ruwa a yan kwanakin nan, ya sanya bakin haure cigaba da kwarararowa kasar Italiya daga Libya.
Ko a ranar Alhamis, sai da majalisar dinkin Duniya ta sanar da isar bakin haure kasar Italiya su 21,666 cikin watanni uku, a haka, shine adadin yan ci rani mafi karanci cikin shekaru hudu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng