Yanzu-yanzu: 'Yan baranda sun tarwatsa taron APC a jihar Ondo, mutane da dama sun jikkata

Yanzu-yanzu: 'Yan baranda sun tarwatsa taron APC a jihar Ondo, mutane da dama sun jikkata

A kalla mutane 50 ne suka ji munanan raunuka a sakamakon harin da 'yan baranda suka kai yayin da wani bangare na jam'iyyar APC ke gudanar da taron ta a jihar Ogun a yau Asabar.

Adadin mutane da suka jikkata yana karuwa a halin yanzu da ake rubuta rahoton nan.

Bangaren na jam'iyyar APC suna taron ne a dakin taro na BTO Hall da ke Illesa road lami-lafiya sai kwatsam wasu da ake kyautata zaton 'yan barandan siyasa ne da suka shigo dakin taron dauke da miyagun makamai kamar bindigogi, adda, barandami da sauransu.

'Yan baranda sun kai hari a taron APC da akeyi a wata jihar Yamma, sun jikkata mutane da dama
'Yan baranda sun kai hari a taron APC da akeyi a wata jihar Yamma, sun jikkata mutane da dama

KU KARANTA: Dubi yadda zaka iya caje 'dan sanda bayan ya tsare ka a hanya ko yazo maka gida - Hukumar 'Yan sanda

An nakada wa shugabanin jam'iyyar duka ciki har da dan majalisa mai wakiltar yankunan Ifedore/Idanre, Honarabul Baderinwa da kuma kwamishinan hadin kan yankuna, Honarabul Bola Ilori.

Wasu 'yan jarida da ke wajen taron sun sha duka ciki har da ma'aikacin jaridar Sun Nwespaper a yayinda yan barandan suka tare kofar fita daga dakin taron don aikata mumunnar aikin su.

A yayin da Honarabul Ilori ya sha da kyar, wasu daga cikin makarabansa sun sha sara a sassan jikinsu daga yan barandan.

Ana zargin cewa 'yan barandan ma'aikatan kungiyar direbobin kasa (NURTW) ne duk da cewa sunyi ikirarin cewa an basu umurni ne daga sama.

Yan barandan sun iso wurin taron ne cikin motoccin bus kuma suka wuce dakin taron kuma sukayi barazanar harbe duk wanda bai basu hadin kai ba duk da cewa akwai wasu gadi a wajen sai dai sun fi karfin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164