Babbar magana: Jami'an tsaro a Najeriya sun kama yahudawa akalla 70

Babbar magana: Jami'an tsaro a Najeriya sun kama yahudawa akalla 70

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa jami'an tsaron Najeriya sun yi nasarar cika hannuwan su da wasu 'yan Najeriya da suke ikirarin cewa suna bin addinin yahudawa a gidan hatsabibin nan Nnamdi Kanu.

Makwaftan gidan na Nnamdi Kanu da yanzu haka ba'a san inda yake ba dai sun ce ranakun Juma'a da Asabar din satin da ya gabata sun rasa samun sukunin yin harkokin su sakamakon ayyukan ibadar da yahudawan ke yi.

Babbar magana: Jami'an tsaro a Najeriya sun kama yahudawa akalla 70
Babbar magana: Jami'an tsaro a Najeriya sun kama yahudawa akalla 70

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta kwace kadadorin Sanata

Legit.ng ta samu cewa daga baya ne dai jami'an tsaron 'yan sandan suka kama su bayan sun yi kokarin tarwatsa su amma hakan ya citura.

A wani labarin kuma, Jami'an rundunar sojojin saman Najeriya watau Nigerian Air Force (NAF) a takaice a jiya sun sanar da samun nasarar yin luguden wuta akan sansanonin 'yan ta'addan Boko Haram a kauyukan da ke garuruwan Bama, jihar Borno.

Kamar dai yadda sanarwar da rundunar ta fitar, sun ce jami'an leken asirin su ne suka gano maboyar ta 'yan Boko Haram din kafin daga bisani suyi masu luguden wuta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng