Makarfi ya bawa Obasanjo shawara kan yadda za'a hambare gwamnatin Buhari a zaben 2019

Makarfi ya bawa Obasanjo shawara kan yadda za'a hambare gwamnatin Buhari a zaben 2019

- Sanata Ahmed Makarfi ya shawarci Obasanjo ya dena sukar PDP da sauran jam'iyoyin adawa

- Makarfi ya ce rabawa kawunan jam'iyoyin adawa zai bawa jam'iyyar APC nasara ne cikin sauki

- Tsohon gwamnan ya ce idan ana son a hambare APC, dole ne jam'iyoyin adawa su hada kansu kamar yadda jam'iyoyin adawa suka yiwa PDP a 2015

Tsohon shugaban rikon kwarya na jam'iyyar PDP, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya shawarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya dena raba kawunnan jam'iyoyin adawa saboda hakan zai bawa jam'iyyar APC daman zarcewa kan mulki ne.

Makarfi ya gargadi tsohon shugaban kasa Obasanjo
Makarfi ya gargadi tsohon shugaban kasa Obasanjo

Makarfi ya ce irin kushe da suka da tsohon shugaban kasar ke nuna wa ga jam'iyyar PDP da sauran jami'iyyun adawa zai zama alheri ne ga jam'iyyar APC wanda hakan zai sa su lashe zaben 2019.

KU KARANTA: Dubi yadda zaka iya caje 'dan sanda bayan ya tsare ka a hanya ko yazo maka gida - Hukumar 'Yan sanda

A cewarsa idan Obasanjo bai hada kai da sauran jam'iyyun adawa don hada karfi da karfe waje guda ba don tunkarar 2019, "Abinda a ke tsoro na tabbatar APC a kan kujerar mulki zai faru saboda halayen na Obasanjo."

Makarfin, wanda tsohon gwamnan jihar Kaduna ne ya yi wannan tsokaci ne a wata zantawa da ya yi da manema labarai a Kaduna bisa yadda tsohon shugaban kasa Obasanjo ya ke sukar duk wata jam'iyya wanda ba nasa ba.

"Muna mutunta shi a matsayinsa na dattijo kuma tsohon shugaban kasa duk da nakasun da ya ke dashi sai dai idan jam'iyoyin adawa ba su hadda kai waje guda ba, babu yadda za'ayi mu kori APC daga mulki. Rashin hadin kanmu ne zai tabbatar da APC kan mulki," inji shi.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa hadin kan da jam'iyyun adawa sukayi a gabanin zaben 2015 inda suka kafa APC ne yasa su kayi nasarar hambare jam'iyyar PDP daga mulki kuma a yanzu idan ba hakan jam'iyoyin adawa su kayi ba, zai yi wuya a kawar da APC daga mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164