Rigar Kowa: Anyi Jana'izar Surukin Obasanjo a jihar Edo

Rigar Kowa: Anyi Jana'izar Surukin Obasanjo a jihar Edo

A ranar Juma'ar da ta gabata ne aka gudanar da jana'iza gami da sanya gawar Dakta Christopher Abebe a makwancinta.

Surukin Obasanjo; Christopher Abebe
Surukin Obasanjo; Christopher Abebe

Marigayi Abebe wanda ya kasance suruki ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya riga mu gidan gaskiya ne a ranar 22 ga watan Maris na wannan shekara yayin da yake shekaru 99 da haihuwa a duniya.

Marigayin ya kuma kasance mahaifi ga tsohuwar matar Obasanjo, Misis Stella Obasanjo, da ita ma ajali ya katse mata hanzari tun a ranar 23 ga watan Oktoba na shekarar 2005 wani hatsarin jirgin sama.

Rahotanni da sanadin shafin jaridar The Punch sun bayyana cewa, an binne gawar surukin tsohon shugaban kasar a mahaifar sa ta garin Iruekpen dake karamar hukumar Esan ta Yamma a jihar Edo.

Legit.ng ta fahimci cewa, Marigayi Ababe ya rike muhimman mukamai da dama a kasar nan da suka hadar da shugaba na jami'ar Najeriya ta Nsukka, Jami'ar Calabar ta jihar Cross River da kuma Jami'ar Benin dake jihar Edo.

Ya kuma rike shugabancin babban kamfanin nan na United African Company Nigeria Limited da kuma mukamai na Limanci a wasu manyan Cocika na kasar nan.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya bayyana abinda Jihar Ekiti ta rasa Karkashin gwamna Fayose

Kamfanin dillancin labarai na najeriya ya ruwaito cewa, an binne gawar Christopher Abebe ne da misalin karfe 3.30 na yammacin ranar Juma'a a daidai makwancin mahaifin sa, Cif Abebe Ogbekhiulu, da riga mu gidan gaskiya a ranar 26 ga watan Oktoba na shekarar 1956.

Mahalarta wannan jana'iza sun hadar da Obsanjo, gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo da kuma takwaransa na jihar Oyo, Abiola Ajimobi tare da mai dakin sa, Florence.

Sauran mahalartan sun hadar da; Sanata mai wakilta jihar Edo ta tsakiya; Clifford Ordia da kuma sauran 'yan majalisar dokoki ta tarayya masu wakilcin jihar Edo gami da tsohon gwamnan jihar, Sanata Oserheimen Osunbor.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel