Dandalin Kannywood: Hadiza Gabon ta yi ma wasu gajiyayyu sha tara na arziki (Hotuna)

Dandalin Kannywood: Hadiza Gabon ta yi ma wasu gajiyayyu sha tara na arziki (Hotuna)

Shahararriyar tauraruwar fina finan Hausa da aka fi sani da suna Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon ta rabar da kayan masarufi ga wasu mutane gajiyayyu dake cikin halin bukata, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Daga cikin abubuwan da gajiyayyun suka samu daga hannun Hadiza akwi shinkafa, Taliya, suga da sauran kayayyakin hatsi, inda aka hangesu cikin farin ciki a yayin da suke kwasar rabonsu, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito

KU KARANTA: Abin kunya: Kwamishinan jihar Borno ya bayyana dalilinsa na raba ma matasa kayan shushaina

Dandalin Kannywood: Hadiza Gabon ta yi ma wasu gajiyayyu sha tara na arziki (Hotuna)
Rabon

Hadiza na daga cikin jarumar Kannywood dake da tausayin gajiyayyu, tare da ganin ta yi kokarin tallafa musu ta hanyar sawwaka musu halin kangin da suke ciki, daga arzikin da Allah ya horee mata.

Da ma ko a baya, jarumar ta saba yin irin wannan kabakin arziki ga jama’a, don a shekarun da suka wuce Legit.ng ta kawo wani rahoto inda Hadiza ta tallafa ma wata yarinya mai suna Rahama wanda ake yawon bara da ita a cikin roba, inda ta bat gudunmwar naira dubu hamsin, sai dai Rahama ta rasu.

Dandalin Kannywood: Hadiza Gabon ta yi ma wasu gajiyayyu sha tara na arziki (Hotuna)
Rabon

Tabbatattun rahotanni sun bada shaidar Hadiza ta sha zuwa sansanonin yan gudun hijira daban daban dake fadin kasar nan, da nufin agaza ma mazaunn sansanonin da kayan abinci, kayan sawa, da ma sauran kayan rufin asiri.

Haka zalika a wani labari makamancin wannan, fitaccen dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa dake taka leda a kungiyar CSKA Moscow, ya raba ma mata kayan abinci da suka hada da shinkafa, taliya da Mai a filin wasansa dake jihar Kano.

Dandalin Kannywood: Hadiza Gabon ta yi ma wasu gajiyayyu sha tara na arziki (Hotuna)
Rabon

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng