Masoyina ne ya yi min ciki ba mijina ba – wata matar aure ta shaidawa kotu cikin alfahari
Wata mata, Marian Folarin, dake sana’ar sayar da biredi ta shaidawa wata kotu dake Mapo a Ibadan cewar, masoyin ta ne ya yi mata ciki ba mijin ta, Kayode Folarin, ba.
Marian, mai ‘ya’ya hudu, ta yiwa kotu korafin cewar mijin nata ya gaza ta fuskar daukan dawainiyar gidan su.
“Mai girma mai shari’a, babu abun da na karu da shi a tsawon zaman shekaru 20 da mijina sai dai yunwa, kishin ruwa, da kaskanci. Ya gaza daukan dawainiya tad a ta yaran mu da muka Haifa amma duk da haka wasu lokutan yana duka na,” a cewar Marian.
Marian ta kara da cewar, mijin ya saba dukkan alkawura da yarjejeniyar da aka yi da shi a gaban kotu, hasali ma t ace ya kauracewa kwanciya da ita tun shekarar 2007 saboda kada ta dauki juna biyu.
“A yanzu haka ina dauke da juna biyu da masoyina, Olalade, mai sana’ar kanikanci a garejin Gate area, Ibadan, ya yi min," Marian ta shaidawa kotu ba tare da shakkar komai ba.
Matar ta roki kotun da ta hana mijin ta, Kayode, cin mutuncin ta ko kokarin musguna mata saboda a cewar ta yanzu bata son sa domin ta samu sabon masoyi.
Sai dai kayoed ya musanta dukkan zargin da matar sa tayi masa tare da shaidawa kotun cewar har yanzu yana son matar sa.
DUBA WANNAN: An yiwa wata mata bulala 75 bayan zaman gidan yari na wata 6 saboda auren mutumin da mahaifin ta ba ya so
A cewar kayode, “mai girma mai shari’a, Marian makarciya ce ajin farko domin ina ba ta kulawa tare da nuna mata soyayya bakin gwargwado. Wasu ne kawai ke hure mata kunne, amma na san ni ne nayi mata ciki ba wani bakanike ba.”
Alkalin kotun ya bukaci a yiwa Marian gwajin juna biyu tare da bayar da umarnin aike sammaci ga saurayin ta, Olalade.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng