Matashi ya burmawa budurwar shi wuka saboda tana zargin sa
Wani matashi, Saliu Ladayo, mai shekaru 24, ya kashe budurwar sa, Confidence Nwamaka, ta hanyar daba mata wuka a ciki.
Saliu ya kashe Nwamaka, mai shekaru 19 dake rubuta jarrabawar kammala sakandire, rabar Talata bayan wani sabani ya shiga tsakanin su.
Jaridar Sahara Reporters ta rawaito cewar lamarin ya faru ne a layin Falodun dake unguwar Oshinle a garin Akure, babban birnin jihar Ondo.
Wani shaidar gani da ido ya ce masoyan sun dade tare duk da suna yawan samun sabani saboda Nwamaka na yawan zargin Saliu da cin amanar soyayyar su.
Shaidar ya ce masoyan sun kaure da fada bayan cacar baki a tsakanin su kuma kafin jama'a su kai agaji tuni ya burma mata wuka. Nwamaka ta mutu yayin da ake kokarin garzayawa da ita asibiti.
Daga baya ne Saliu ya shaidawa jama'a cewar, zagi da tsinuwar da Nwamaka ke yi masa a kan kula wasu 'yan matan ya hada su fada.
DUBA WANNAN: Kwankwaso ba zai iya kayar da Buhari a Kano ba - El-Rufa'i
Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Ondo, Femi Joseph, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewar tuni sun kama matashin kuma tuni ya amsa laifin sa.
Iyayen yarinyar sun roki 'yan sanda da su gudanar da binciken kwakwaf tare da tabbatar da na bi masu hakkin kisan diyar su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng