Jinjina ga Almajiri ajin Farko: Alhaji Isiyaka Rabi'u

Jinjina ga Almajiri ajin Farko: Alhaji Isiyaka Rabi'u

- Idan za'ayi rubutu akan wanda yake da baiwa kala kala, sai mutum ya rasa ta inda zai fara

- Khalifa masanin addini ne, dattijo ne wanda ake ganin girman shi

- Ance an haifeshi ne a 1928, amma mutane da yawa sunce shekarun shi 95 a duniya

Jinjina ga Almajiri ajin Farko: Alhaji Isiyaka Rabi'u
Jinjina ga Almajiri ajin Farko: Alhaji Isiyaka Rabi'u

Khalifa shehi Isyaku Rabiu ya zama mutum mai baiwa kala kala a Najeriya. Mahaddacin Qur'ani ne, baiwar da tafi kowacce girma. Sanannen Dan kasuwa ne kuma magidanci ne.

Magajin Muhammadu Rabiu, mahaifin shi, shehi Muhammadu Rabiu shima sanannen malami ne kuma mahaddacin Qur'ani.

Khalifa Isyaku Rabiu, wanda muke kira da Alhaji Babban, shi ne sanannen danshi amma sauran 'ya' yan nashi ma malamai ne. Masanan Qur'ani ne: sun hada da marigayi Alhaji Yusuf Rabiu, marigayi Malam Zubairu Rabiu, marigayi Alhaji Bala Rabiu, Gwani Tijjani Rabiu, Malam Almustapha Rabiu, marigayi Malam sabiu Rabiu da Alhaji Shehu Rabiu duk mahaddatan Qur'ani mai girma ne.

A gurin hidimar addini kuwa, ya hidimtawa bangaren Tijjaniya, an nada shi Khalifa ne a tsakiyar 90's.

Khalifa ya rayu ne akan hidimtawa Qur'ani mai girma, masu koyon shi da kuma musulunci baki daya.

A wannan ta'aziyyar tashi, zan fadawa matasa yan'uwana halayen shi guda biyu da ya dace muyi koyi.

DUBA WANNAN: Dirar mikiya ga 'yan shi'a

Na farkon, ganin Khalifa ba sai an cike wasu sharudda ba, ballantana a ranakun juma'a bayan sallar. Abinda ya kamata muyi koyi shine, duk da matsayin shi, abokan shi da dangin shi suna ziyartar shi a ko.

Na biyu daga cikin halayen shi da ya kamata muyi koyi dashi shi ne, ba ya taba kyamatar mutane. Yana da karamci ga mutane ba tare da bambanci ba. Shiyasa zaka ga manyan malamai daga bangarori da dama na addini ke kawo mishi ziyara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng