Majalisar Malaman Musulunci sun yi Allah-wadai da aikin Gwamna El-Rufai
- Majalisar Malaman Kaduna sun yi Allah-kyauta da aikin Gwamnan Jihar
- Sheikh Usman Baban-Tine yace sam bai dace Gwamna ya rika tsinuwa ba
- Babban Malamin yake cewa tsinuwa idan ta fita ba ta faduwa kasa banza
Mun samu labari cewa Majalisar Malaman addinin Musulunci na Jihar Kaduna sun yi Allah-wadai da abin da Mai girma Gwamnan Jihar yayi na tsinewa wasu ‘Yan Majalisar Jihar albarka kwanakin baya.
Kamar yadda labari ya zo mana Shugaban Majalisar Malaman Jihar Sheikh Usman Abubakar Baban-Tine yayi jawabi a gaban ‘Yan jarida a makon nan inda yace kalaman Gwamnan Jihar na kwanakin baya sam ba su dace ba kuma su na da hadari.
Usman Baban-Tine take cewa a matsayin su na Malamai masu fadar gaskiya dole su fito su yi tir da wannan danyan aiki na Gwamna Nasir El-Rufai. Babban Malamin yace bai dace tsinuwa ta rika fitowa daga bakin Shugabanni da ke mulki ba.
KU KARANTA: An nemi Kotu ta janye belin Sanatan Kogi Dino Melaye
Shehin Malamin yake cewa a maimakon a rika kokarin kawo abin da zai kawar da fitina sai kuma a rika jin Mai Girma Gwamna na neman tada-zaune tsaye domin manufar siyasa ba daidai bane. Sheikh Baban-tine yace tsinuwa ba ta fadi kasa banza.
Kwanaki dai Gwamnan na Kaduna ya tsinewa Sanatocin Jihar saboda sun hana a ba Jihar Kaduna damar cin bashi a bankin Duniya. Sai dai masu kare Gwamnan sun ce dama dai duk mutum ajizi ne kuma zai fi kyau a ba Gwamnan shawara a sirri.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng