Kasar Amurka ta aike da sakon Azumi ga musulmin Duniya
Kasar Amurka ta aike da sakon taya murna da fatan alheri ga dukkan musulmin duniya a yayin da za su shiga wata mai alfarma na Ramadana.
Sakataren gwamnatin kasar Amurka, Mike Pompeo ne ya bayar da wannan sakon a watan sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
"A madadin gwamnatin kasar Amurka, ina mika sakon fatan alheri ga daukakin al'ummar musulmi da ke fadin duniya a yayin da za su fara azumin watan Ramadan.
KU KARANTA: Lafiya jari: Abubuwa 6 da mai ciwon ulcer ya kamata ya kiyaye lokacin azumi
"Ga wadanda za su azumci wannan watan, lokaci ne na kara kusanci ga Ubangiji, kyauta da kuma ayyukan alhkairi.
"Ramadan kuma lokaci ne da mutane ke kara kyautata zumuncin da ke tsakaninsu ta hanyar ziyarar 'yan uwa da abokan arziki," inji Pompeo.
A cewar Pompeo, Ramadan lokaci ne da musulmi ke taimakawa marasa karfi ta hanyar sadaka da kyauta.
Musulmi a kasar Amurka da sauran sassan duniya suna bayar da taimako sosai a garuruwan da suke zaune kuma miliyoyi daga cikinsu za suyi amfani da watan wajen kyautata wa makwabtansu da sauran 'yan uwa da abokan arziki.
Pompoe kuma ya ce duk shekara, ofishin jakadar Amurka tana shirya liyafa idan watan azumin watan Ramadan ya kama don kara hadin kai da zaman lafiya tsakanin mutane mabiya adinai daban-daban.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng