Muhimman alkalumma 8 da ya kamata ka sani dangane da sabon babban ofishin EFCC

Muhimman alkalumma 8 da ya kamata ka sani dangane da sabon babban ofishin EFCC

A ranar Talata 15 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddaar da wata katafariyar sabuwar babban ofishin hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin aksa zagon kasa, EFCC a babban birnin tarayya Abuja.

Legit.ng ta zakulo muku wasu muhimman bayani dangane da wannan katafaren ginin zamani da hukumar EFCC ta kammala aikin gininsa akan kudi naira biliyan 24.

KU KARANTA: Kalli yadda Buhari ya kirge makudan dalolin da hukumar EFCC ta kwato daga hannun barayin gwamnati

1-An fara gina ofishin a shekarar 2010 a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

2- Shekaru uku aka yi yarjejeniyar kammala shi, amma aka samu akasi har sai da ya kai shekaru 7

Muhimman alkalumma guda 5 da ya kamata ka sani dake tattare da sabon babban ofishin EFCC
Sabon babban ofishin EFCC

3- Naira biliyan 25 aka kashe wajen gina katafariyar shelkwatar na hukumar EFCC

4- An ginata ne akan hanyar zuwa filin sauka da tashin jirage na Abuja, kmar yadda ofishin FBI na Amurka yake

5- Sabuwar shelkwatar ta EFCC gidan sama ne mai hawa 10

6- Ofishin za ta dauki adadin maaikatan hukumar dai da har guda 700

7- Daga fara ginin zuwa kammala shi EFCC ta samu shuwagabannin uku

8- Katafaren ginin na kunshe da dakin bincike na kimiyya, asibiti, dakunan tsare masu laifi, sashi tsaro, sashin yan kwana kwana, wajen ajiye motoci na karkashin kasa.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin kaddamar da ofishin sun hada da Kaakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu Thabo Mbeki, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele da sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng