Ronaldo na fuskantar matsala kasar Spain, Madrid ta gaza taimakon sa

Ronaldo na fuskantar matsala kasar Spain, Madrid ta gaza taimakon sa

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dake rike da kambun dan wasan Duniya (Ballon d'Or) na cikin halin tsaka mai wuya da hukumomin a kasar Spain bisa biyan kudin haraji.

Kasar Spain ta kakabawa Ronaldo tarar Yuro miliyan 13 bayan ta ce ta same shi da laifin yin amfani da wani kamfani domin boye takamaiman adadin kudin da yake samu.

Ronaldo ya roki kungiyar sa ta Realmadrid da ta taimaka ta biya masa tarar.

Ronaldo na fuskantar matsala kasar Spain, Madrid ta gaza taimakon sa
Ronaldo

Saidai fa kungiyar Real Madrid tayi mursisi tare da yin kunnen uwar shegu a kan wannan bukata ta Ronaldo.

Muddin Ronaldo yana son kubuta daga zuwa gidan yari, dole ya biya gwamnatin kasar Spain adadin miliyan €13.

DUBA WANNAN: Kasar Saudiyya ta bayyana ranar da za a fara azumi a fadin Duniya

Ronaldo ne dan wasa na biyu a cikin jerin 'yan wasan kwallon kafa na duniya da suka fi daukan kudi. Kungiyar Madrid na biyan Ronaldo $340,000 duk sati.

Kasar Spain ta taba zargin dan wasan kungiyar Barcelona, Lionel Messi, da aikata irin wannan laifi tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari duk da dai daga bisani an juya hukuncin zuwa tara wacce dan wasan ya biya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel