Saudiyya ta bayyana ranar da za a tashi da azumi a fadin Duniya
Kasar Saudiyya ta bayyana cewar za a tashi dea azumin watan Ramadan ranar Alhamis mai zuwa a fadin duniya baki daya.
Ba a samu gani jaririn watan Ramadan a yammacin yau, Talata, ba a saboda haka ba za a tashi da azumi gobe, Laraba, ranar karshe a watan Shaaban, ba, kamar yadda hukuma ta sanar a kasar.
Kazalika wasu kasashen Musumi da suka hada da Jordan da Iraq sun bayyana ranar Alhamis a matsayin ranar da za fara azumin watan Ramadan.
Azumin watan Ramadan na daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng