Azumin watan Ramadana: An yi kira ga Malamai game da zage zage yayin fassara Al-Qur’ani

Azumin watan Ramadana: An yi kira ga Malamai game da zage zage yayin fassara Al-Qur’ani

A yayin da azumin watan Ramadan ke karatowa, hadaddiyar kungiyar Musulman Najeriya, JNI, ta yi kira da babban murya ga Malaman addinin Musulunci da su guji furta kalaman batanci da zage zagen juna a yayin da suke fassara Al-Qur’ani.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ce ta ruwaito shugaba Jama’atu, reshen jihar Kogi, Usman Bello ne ya yi wannan gargadi a ranar Talata 15 ga watan Mayu yayin wani taron manema labaru da suka shirya a garin Lokoja.

KU KARANTA: Dakarun Sojojin Najeriya sun bankado wani sansanin yan bindiga dake boye a Nassarawa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Bello ya yi kira ga Malaman addinin Musulunci da su kaurace ma furta munanan kalamai ga juna a yayin tafisiri ko kuma a yayin da suke huduba, inda yace kada su yi abinda zai janyo matsalar tsaro ko kuma ya kasance cin zarafin wasu mabiya addinai.

Bugu da kari, Bello ya nemi a maimakon furta kalaman batanci, kamata ya yi su ta’allaka karatukansu akan cin hanci da rashawa, lalacewar mulki, matsalar tsaro, zalunci, da sauran matsalolin da suka addabi al’ummar kasar.

“Ya kamata Malamai su guji fassara Qur’ani don dacewa da son ransu ko kuma don burge almajiransu, haka zalika su guji yin amfani da Qur’ani wajen cin mutucin mutane.” Inji Bello, wanda tsohon jakadan Najeriya ne a kasar Sudan.

Daga karshe Bello ya yi kira ga Musulmai su yi amfani da watan Ramadana wajen yi ma shuwagabannin kasar Addu’a, tare da addu’ar hadin kai, samun zaman lafiya da cigaba mai daurewa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel