Wani farfesa masanin tarihi ya bayyana yadda Buhari ya yiwa tsohon gwamnan jihar Ondo daurin huhun goro
- Wani aminin maraigayi Obafemi Awolowo ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari bata tabukka wani abin azo-a-gani ba
- Farfesa Banji Akintoye ya bayar da labarin yadda gwamnatin shugaba Buhari ta garkame marigayi tsohon gwamnan Ondo, Adekunle Ajasin duk da cewa yana da gaskiya
- Farfesan ya ce mutane da dama sunyi tsamanin cewa shugaba Muhammadu Buhari zai kawar da cin hanci a Najeriya
Wani masanin tarihi mai shekaru 83 kuma amininin marigayi Cif Obafemi Awolowo, Farfesa Banji Akintoye ya bayar da labarin yadda shugaba Muhammadu Buhari ya kama shi kuma ya garkame shi a kurkuku tare da manyan shugabani kamar marigayi Michael Adekunle Ajasin.
A baya Akintoye ya rubuta budadun wasiku guda biyu zuwa ga shugaba Muhammadu Buhari lokacin yana dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC inda ya zargi shi da tsare shi a kan laifin da bai aikata ba.
A wata hira da ya yi da jaridar Punch, Akintoye ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari bata tabuka wani abin alfahari ba a dukkan fanonin ayyukan gwamnati.
Ga wasu daga cikin abinda Akintoye ya ce: "A yayin da Buhari ya dare kujeran mulki a Disambar 1983, ya kama 'yan siyasa da dama wai saboda yana zarginsu da cin hanci da sauransu. Amma nayi mamakin yadda ya kama ni da wasu takwarori na 'yan jam'iyyar Unity Party of Nigeria wadd a lokacin kowa ya san muna yaki da cin hanci. A lokacin ni sanata ne kuma ina yaki da cin hanci a majalisar dattawa, majalisar wakilai har ma da jihohi.
KU KARANTA: Bamu san cin hanci ba lokacin da nayi mulki - Gowon
"Kowa ya sani cewa mu masu yaki da cin hanci ne kuma ba abinda da muka sa a gaba ila inganta rayuwar mutane, saboda haka idan mutum yana sin yaki da cin hanci ba mu ya kamata ya kama ba. Kawai yana son ya sa mu a kurkuku ne sai dai ni rayuta bana boye-boye hakan yasa baiyi tasiri a kai na ba amma wasu abin bai zo musu da sauki ba.
"Misali kamar Cif Adekunle Ajasin, mutum ne tsoho amma ya zama gwamnan jihar Ondo. Shima mutum ne mai kyaman cin hanci. Akwai wasu labarai da ake bayarwa kansa. A lokacin ne sojoji suka kirkiro kudin tsaro da ake baiwa gwamnoni amma shi bai amince dashi ba. Ya ce shi a matsayinsa na Bayarabe kuma dan jihar Ondo ba zai karba wannan kudi ba."
Akintoye ya cigaba da cewa a wannan zamanin, Cif Ajasin bai tara tara arziki ba, gida daya kawai ya mallaka a Owo wanda ya gina tun yana Principal din. A lokacin har ba'a ake masa a jihar Ondo saboda an san adadin manyan rigunan da ya mallaka.
Akintoye ya ce shugaba Buhari ya sanya anyi bincike har sau uku akan Cif Ajasin amma ba'a same shi da laifi ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng