Kananan hukumomi biyar da PDP ta bawa APC mamaki a zaben jihar Kaduna
A jiya litinin ne hukumar zaben jihar Kaduna (SIECOM) ta bayyana cewar ta sakamakon zaben karamar hukumar bai kammalu ba, kamar yadda kamfanin dillancin Najeriya (NAN) ya rawaito.
Baturen zabe a karaamar hukumar Chikun, Samuel Ndams, ya bayyana cewar sakamakon mazabu bakwai ne daga cikin mazabu 12 ya shigo hannun sa.
Mista Ndams y ace sakamakon mazabu biyar ya shigo hannun sa ba a wurin tattara sakamako ba amma bayan ya tuntubi shelkwatar SIECOM sai ta bayar da shawarar a bayyana sakamakon da cewar bai kammalu ba.
Sakamakon da hukumar zaben ta fitar ya nuna cewar jam’iyyar APC ta lashe kananan hukumomi 12, yayin da jam’iyyar PDP ta lashe zabe a kananan hukumomi biyar, sannan an dakatar da sakamakon kananan hukumomi uku.
Kananan hukumomin da APC tayi nasara sune; Kubau, Giwa, Ikara, Lere, Sabon Gari, Igabi, Kaduna ta Arewa, Zaria, Soba, Makarfi, da Birnin Gwari.
DUBA WANNAN: An kama mabiya Shi'a 60 bayan raunata 'yan sanda biyu
PDP tayi nasara a kananan hukumomin; Jema’a, Zangon Kataf, Kachia, Sanga, da Kauru.
Kamfanin dillanci labarai y ace bai samu sakamakon kananan hukumomin Kagarko da Kajuru ba, yayin da ake cigaba da jiran sakamakon zaben karamar hukumar Kaduna ta kudu.
A yayin da jam’iyyar APC ta bayyana gamsuwar tad a sakamakon zaben kananan hukumomin, jam’iyyar PDP tayi korafin cewar an tafka magudi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng