An bayar da belin matar dan siyasar jihar Borno da tayi barin ciki a hannun ‘yan sanda

An bayar da belin matar dan siyasar jihar Borno da tayi barin ciki a hannun ‘yan sanda

A jiya litinin ne wata babbar kotu a jihar Borno ta bayar da belin, Sa’adatu Muhammad, matar fitaccen dan siyasa a jihar Borno, Grema Terab.

Kazalika kotun ta bayar da belin Karin wasu mutane 20 a kan Naira N100,000 da aka tsare su tare da Sa’adatu tsawon wata guda.

‘Yan sanda sun kama Sa’adatu ne a gidan mijin ta tun watan da ya wuce saboda taki sanar da hukuma kisan kai da aka yi a gidan su yayin wani taron siyasa da mijin ta ya hada.

Hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewar saida ta gargadi dan siyasar, Mista Terab, dan jam’iyyar PDP cewar ya hakura da batun taron day a kira ranar 15 ga watan Afrilu saboda gujewar barkewar rikici amma ya yi kunnen uwar shegu da shawarar.

An bayar da belin matar dan siyasar jihar Borno da tayi barin ciki a hannun ‘yan sanda
Gwamnan jihar Borno; Kashim Shettima

Saidai Mista Terab ya shaidawa Jaridar Premium Times cewar zancen hukumar ‘yan sandan ba gaskiya bane tare da kalubalantar su da su bayyana hujjar hakan ta faru.

Mista Terab, tsohon shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Borno, ya ce anyi taron day a shirya an gama lafiya amma bayan magoya bayan sa sun tafi sai wasu ‘yan daba suka zo suka tayar da husuma.

DUBA WANNAN: An kubutar da jarirai 24 a wani haramtaccen gidan ajiye jarirai a Legas

Matar Mista Terab, Sa’adatu, tayi barin juna biyu da take dauke das hi kwana daya kacal bayan an garkame ta a ofishin ‘yan sanda cikin yanayi mai tsanani.

Jigo a PDP, Atiku Abubakar, ya yi alla-wadai da kama matar Mista Terab tare da bayyana hakan da cewar amfani ne da iko ta hanyar da bai dace ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel