Falasdinawa sunyi Allah wadai da komawar Ofishin jakadancin Amurka Qudus

Falasdinawa sunyi Allah wadai da komawar Ofishin jakadancin Amurka Qudus

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya jinjiinawa ofishin jakadancin Amurka akan kokarin da suka yi wurin mayar da ofis din su birnin Qudus

Falasdinawa sunyi Allah wadai da komawar Ofishin jakadancin Amurka Qudus
Falasdinawa sunyi Allah wadai da komawar Ofishin jakadancin Amurka Qudus

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya jinjiinawa ofishin jakadancin Amurka akan kokarin da suka yi wurin mayar da ofis din su birnin Qudus. Yace wannan ranar farin ciki ce a tarihin Isra'ila ga taron mutane wurin 800 wanda ya kunshi manya-manyan masu fada a ji a duniya.

DUBA WANNAN: Labari mai dadi: Kasar Canada zata maida Najeriya ta daya a harkar hako ma'adanai

Anyi taron ne a ranar Litinin bayan da aka kashe masu zanga zangar lumana 'yan kasar Pakistan da kuma sama da mutane 2,400 da suka ji raunuka sakamakon jami'an tsaron Isra'ila da suka bude musu wuta a Gaza.

A lokacin da yake jawabi a sabon ofishin jakadancin Amurkan da aka gina a birnin na Qudus, Netanyahu ya jinjinawa shugaban kasa Donald Trump domin ya cika alkawarin kamfen da yayi na maida ofishin jakadancin daga Tel Aviv. Yace dangartakar dake tsakanin kasashen biyu mai karfi ce har abada.

"Shugaba Trump, Idan muka duba tarihi, zamuce kaima ka kafa tarihi." inji firayem ministan Isra'ila.

"Wannan rana ce ta farin ciki a gare mu, ta kwanciyar hankali kuma. Da zaman lafiya kadai gaskiya ke tabbata, kuma gaskiya birnin Qudus shine babban birnin kasar Isra'ila a kusan shekaru 3,000."

Kalamanshi basu yi ma wasu dadi ba, kamar su ministan harkokin waje na Faransa Jean-Yves Le Drian, wanda yace maida ofishin jakadancin ya sabawa dokar kasashen.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel