An kubutar da jarirai 24 a wani haramtaccen gidan raino a Legas

An kubutar da jarirai 24 a wani haramtaccen gidan raino a Legas

A jiya ne gwamnatin jihar Legas ta rufe wani haramtaccen gidan rainon yara mai suna Pro Labore Der a yankin Olorunda a Badagary, tare da bayyana kubutar da yara 24.

Ma’aikatar matasa da walwalar jama’a ce ta rufe gidan bayan samun kiran gaggawa a kan gidan da yadda suke gudanar da harkokin su. Mai haramtraccen gidan ya tsere kafin jami’an tsaro su kai wurin.

Duk da guduwar shugaban gidan, jami’an gwamnati sun yi nasarar ceto wasu jarirai da basu wuce watanni hudu ba tare da wata ‘yar shekaru 17 dake dauke da juna biyu.

An kubutar da jarirai 24 a wani haramtaccen gidan raino a Legas
An kubutar da jarirai 24 a wani haramtaccen gidan raino a Legas

Da yake ganawa da manema labarai a kan samamen da suka kai gidan, kwamishinan ma’aikatar matasa da walwalar jama’a na jihar Legas, Agboola Dabiri, ya bayyana cewar gwamnatin jihar Legas ba zata taba komawabaya a kudirin tan a ganin ta rufe dukkan haramtattun gidajen raino ba tare da bawa masu sha’awar bude irin wadannan gidaje dasu yi rijista da gwamnati.

DUBA WANNAN: Matashi ya yi zigidir sannan ya haye kan hasumiyar masallaci a Kano

Saud a dama an sha rufe irin wadannan gidaje a Legas tare da kama masu gidajen. Rahotanni sun sha bayyana cewar jariran basa samun wadatacciyar kulawa ta fuskar muhalli, abinci, sutura da kulawa da lafiyar su.

Kazalika Dabiri ya bayyana cewar babu wani addini da yake da ikon bayar da izinin bude gidan raini ga kowa tare da bayyana cewar ma’aikatar sa ce kadai keda wannan iko.

A karshe ya shawarci masu gidajen haya das u saka idanu sosai domin tabbatar da abinda ‘yan hayar gidajen su ke aikatawa domin gudun bawa masu laifi mafaka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng