El-Rufai yayi na'am da zaben kananan hukumomin jihar Kaduna
- Yayinda gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasir El-Rufai yace yayi na'am da zaben kananan hukumomin jihar da aka gudanar tare da cewa jam'iyyarsa ta lashe arewaci da tsakiyar jihar
- Ita kuwa babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta nuna korafin ta inda tace an yi rashin gaskiya a zaben
Duk da irin jinkirin da aka samu na bayyana sakamakon zaben kananan hukumomin jihar ta Kaduna tare da soke sakamakon wasu wuraren zaben, gwamnan jihar Kadunan Mal. Nasiru El-Rufai yace an samu nasara tunda an yi zaben ba tare da wani tashin hankali ba.
DUBA WANNAN: Gwamnatin Buhari ba abinda ta tsinanawa Al'umma - Shekarau
A cewar sa anyi zaben na na'ura mai kwakwalwa lafiya ba tare da an jiwa wani ciwo ko an kashe wani ba. Yace akwai magudi da aka samu bayan an kammala zaben saboda haka ba'a fitar da duka sakamakon zaben ba. Yayi kira ga al'ummar jihar da suyi hakuri kafin a bayyana sauran sakamakon.
Yace al'ummar jihar sun nuna zasu iya shiga layi su yi zabe ba tare da fada da junansu ba lamarin da yayi ikirarin ya zama misali ga Najeriya da ma Afirka baki daya. Gwamnan ya godewa al'ummar jihar a bisa kokarin da suka nuna.
A cewar sa zaben ya nuna talakawan jihar sun fahimci cewa gwamnatin sa tana yi musu aiki domin kuwa jam'iyyar sa ta lashe kananan hukumomin arewaci da tsakiyar jihar yayin da wasu jam'iyyu na adawa suka lashe kudancin jihar.
Sai dai kuma ganin jikirin da aka samu da soke zabuka da aka yi a wasu wuraren yasa shugaban babbar jam'iyyar adawa PDP na jihar Felix Hassan ya kira taron manema labarai inda yace jam'iyyar sa tana da wasu korafe-korafe akan zabukan. A cewarsa wasu jami'an zabe sun bace amma kuma sai gashi ana bada sakamakon zabukan. Akwai wuraren da ba'a yi zabe ba amma an ce jam'iyyar APC ta ci zaben wuraren. Ya sha alwashin bin duk hanyoyin da doka ta tanada domin ganin sun yaki abun dake faruwa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng