Mutane hudu sun mutu a wata arangama tsakanin jami’an kwastam da ‘yan sumogal

Mutane hudu sun mutu a wata arangama tsakanin jami’an kwastam da ‘yan sumogal

A kalla mutane hudu ne suka mutu yayin da wasu shida suka samu raunuka bayan musayar wuta tsakanin jami’an kwastam da masu sumogal a Ilara dake karamar hukumar Imeko-Afon a jihar Ogun.

Rahotanni sun bayyana cewar lamarin ya faru ne da misalign karfe 8:30 na safe a kan iyakar Najeriya da kasar Benin.

An samu barkewar rikicin ne yayin da ‘yan sumogal din suka yi kwamba domin raka shinkafar da suka shigo da ita ya zuwa garin Abeokuta, amma suka yi kacibus da tawagar jami’an tsaro, da ta hada da sojoji da jami’an kwastam, dake yaki da sumogal.

Mutane hudu sun mutu a wata arangama tsakanin jami’an kwastam da ‘yan sumogal
Jami’an kwastam

‘Yan sumogal din sun tirje a lokacin da jami’an tsaro suka yi kokarin kwace shinkafar da suka shigo da ita, sanadin day a kai ga musayar wuta a tsakanin su da tayi sanadiyar mutuwar mutane hudu, wasu shida kuma suka samu raunuka.

DUBA WANNAN: An kulle iyaye da waliyyin amarya saboda taki tarewa gidan ango

Kakakin hukumar Kwastam a jihar Ogun, Abdullahi Maiwada, ya tabbatar da faruwar lamarin, saidai bai bayar da adadin mutanen da suka mutu ba sakamakon musayar wutar.

Na san cewar an samu matsala tsakanin jami’an mu da wasu dake fasakwabrin shinkafa a kan iyakar Ilara a lokacin da suke kokarin shigowa da motocin shinkafa. Saidai bani da cikakken bayanin abinda ya faru amma da na samu bayani zan sanar da ku,” a cewar Maiwada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel