Jam'iyyar adawa PDP ta koka da zaben kananan Hukumomin Kaduna

Jam'iyyar adawa PDP ta koka da zaben kananan Hukumomin Kaduna

Jam'iyyar PDP ta ba ta amince da zaben da aka gudanar a karshen makon nan a Jihar Kaduna ba. Sakataren yada labarai Kola Ologbondiyan yace an yi murdiya. Wannan karo dai an yi amfani ne da na’ura mai kwakwalwa wajen zaben Kananan Hukumomin.

An koka da sakamakon zaben da aka gudanar a Ranar Asabar a wasu wuraren. Akwai inda aka sanar da cewa APC tayi nasara duk da ba a sanar da sakamakon zaben a inda aka kada kuri'a ba. Wasu masu aikin zaben ma dai sun tsere.

Daily Trust ta rahoto cewa Ma’aikatan zabe na Jihar Kaduna KADSIECOM sun bar ofisoshin yayin da aka nemi su yi magana da ‘Yan jaridu. Jam’iyyar APC ce tayi nasara a Kananan Hukumomi 10 na Jihar inda mu ke jin PDP tayi nasara a 3.

KU KARANTA: An saki zaben Kananan Hukumomin Jihar Kaduna

Sai dai Jam’iyyar adawa ta koka da cewa sam ba ta yarda da sakamakon zaben ba inda tace an yi murdiya. PDP tace abin da ya faru a layin zabe dabam, sannan kuma abin da aka sanar a matsayin sakamakon zabukan Jihar dabam.

Wata Majiyar mu ta bayyana mana cewa yayin da Mutanen Gari su ke jira a sanar masu da sakamakon zabe a Kauyuka sai dai kurum su ka ji labari a gidajan rediyo da kafofin sadarwa cewa APC tayi nasara a zaben na Ranar Asabar da ta gabata.

Kafin nan kun ji labari cewa an rasa inda Ma’aikatan zaben da su kayi aiki a irin su Karamar Hukumar Kaduna da Kudu, Kajuru, Kagarko, Chikun, Jemaa, Sanga da sauran su su ka shige.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel