Matsafa sun sako Maiduguri a gaba: An kashe budurwa da wata yarinya, an kwakule idanun wani dattijo

Matsafa sun sako Maiduguri a gaba: An kashe budurwa da wata yarinya, an kwakule idanun wani dattijo

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Borno, Damian Chukwu, ya bayyana cewar sun fara bincike a kan aiyukan matsafa dake barazana ga mazauna garin Maiduguri domin yiwa tufkar hanci.

Kwamishinan ‘yan sandan ne ya bayyana haka ne ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) yau, Lahadi, a Maiduguri.

Mista Chukwu ya bayyana cewar jami’an hukumar na binciken laifukan kisan wata budurwa a watan day a gabata da kuma kwakulewa wata dattijuwa mai 58, dake da tabin hankali, idanu da ake zargin masu yin tsafi da sassan mutum da aikatawa.

Matsafa sun sako Maiduguri a gaba: An kashe budurwa da wata yarinya, an kwakule idanun wani dattijo
gwamnan jihar Borno; Kashim Shettima

An tsinci gawar budurwar a dakin wani Otal a Maiduguri bayan an yi mata yankan rago, kamar yadda kwamishina Chukwu ya bayyana.

NAN ta rawaito cewar jama’ar rukunin gidajen 202 dake garin Maiduguri sun shiga halin dimuwa da juyayi biyo bayan kwakule idon wani mutum, ta karfin tsiya, dan gudun hijira dake zaune a unguwar.

DUBA WANNAN: Buhari zai kai ziyara jihar Jigawa, an baza jami'an NSCDC 2,000

Majiyar NAN ta bayyana mata cewar, kwakule idanun mutumin na zuwa ne kwana daya kacal bayan tsintar gawar wata karamar yarinya mai shekaru bakwai a unguwar Mairi dake cikin garin Maiduguri.

Wani mazaunin rukunin gidajen 202, Gulumba Galtimari, ya shaidawa NAN cewar wasu mutane ne suka danne mutumin ta karfin tsiya suka kwakule masa idanu da wani karfe mai kaifin gaske.

Galtimari ya kara da cewa, “mun samu mutumin yana ta ihu cikin ciwo. Duk kokarin mu na sanin sunan sa ko inda ya fito yaci tura.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel