Zaman kadaici ya sa wata Baiwar Allah ta auri kan-ta amma ta kare da cin-amana

Zaman kadaici ya sa wata Baiwar Allah ta auri kan-ta amma ta kare da cin-amana

- Kwanakin baya wata Budurwa ta auri kan-ta bayan ta gaji da jiran miji

- Sai dai yanzu auren wannan Budurwa mai mamaki na nema ya wargaje

- Ana zargin Sophie Tanner da yin wani sabon saurayi bayan da tayi aure

Mun samu labari daga Kasar waje cewa wata Baiwar Allah mai shekaru kusan 40 da ta auri kan ta kwanakin baya ta saba alkawarin da tayi da kan ta. Sai dai kuma wannan Budurwar mai suna Sophie Tanner tayi abin assha daga baya.

Zaman kadaici ya sa wata Baiwar Allah ta auri kan-ta amma ta kare da cin-amana
Tanner ta fara yawo da wani saurayi bayan ta auri kan ta

Jaridar Metro ta rahoto cewa Sophie Tanner ta ci amanar kan-ta yayin zaman wannan aure mai ban mamaki. Da farko dai Sophie tayi alkawari ba za ta sadu da kowa ba a lokacin da ta auri kan ta amma sai ga shi kamar ta saba hakan da kan ta.

KU KARANTA: Wata 'Yar Baiwa ta ci kyautar Dala $4000 a Legas

Shekaru 2 da su ka wuce ne aka yi wannan aure a Turai inda tace mutu-ka-raba, yanzu dai an samu labari cewa Sophie Tanner tayi wani wani Saurayi mai suna Ruari Barrett. Barret dai Tazuru ne wanda bai da Iyali don haka ake zargin da-walakin.

Kwanakin baya dama kun ji cewa wannan Budurwa ta auri kan-ta inda ta rantse cewa mutu-ka-raba takalmin kaza. Ba dai wannan karo bane aka fara samun mace ta auri kan-ta a Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng