Bajiman Shehunan addinin Musulunci da su ka riga mu gidan gaskiya a watan nan

Bajiman Shehunan addinin Musulunci da su ka riga mu gidan gaskiya a watan nan

Daga cikin ‘yan makonnin nan an yi rashin manyan Malaman addinin Musulunci a Najeriya. Don haka ne mu ka kawo jerin wadannan rashi da aka yi yayin da al’ummar Musulmai a Duniya ke shiryawa azumin Watan Ramadana.

Bajiman Shehunan addinin Musulunci da su ka riga mu gidan gaskiya a watan nan
Lokacin da aka shigo da gawar Isiyaka Rabiu

1. Sheikh Isiyaka Rabiu

Shehin Malamin Musulunci Isiyaka Rabiu ya rasu a makon da ta gabata a Landan yana da shekaru kimanin 90. Malamin yayi shekara da shekaru yana yi wa Musulunci aiki a Afrika da ma daukacin Duniya.

KU KARANTA: Akuyar Najeriya ta dauke hankulan jama'a a kasar waje

2. Sheikh Imam Lawal

A makon da ya wuce dai kun ji cewa babban Limamin Masallacin Garin Katsina Imam Muhammad Lawal ya rasu yana da shekaru 95 a Duniya. Malamin yayi shekaru da dama yana limanci a Garin.

3. Sheikh Yahuza Waziri

A makon jiya ne kuma aka rasa Shehin Malamin nan Yahuza Balarabe Waziri na Birnin Zazzau. Sheikh Yahuza shi ne Na’ibin Zazzau wanda ya kan yi Limanci ko yaushe a Masallacin gidan Sarki. Ya rasu yana da shekaru 77.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel