'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 56 da ake zargi da kai harin Birnin Gwari

'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 56 da ake zargi da kai harin Birnin Gwari

Hukumar Yan sandan Najeriya sunyi nasarar cafke 'yan bindiga da 'yan sara suka 56 wanda ake zarginsu da hannu cikin kashe-kashen da akayi a garin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna da ma wasu sassan jihar Zamfara.

Wasu daga cikin wandanda aka kama sun hada da Abdullahi Abubakar, 35 (shugaban kungiya); Halidu Musa, 34; Mohammed Ruwa, 30; Mohammed Sani, 30; Dahiru Yahaya 38 kamar yadda kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito.

'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 56 da ake zargi da kai harin Birnin Gwari
'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 56 da ake zargi da kai harin Birnin Gwari

'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 56 da ake zargi da kai harin Birnin Gwari
'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 56 da ake zargi da kai harin Birnin Gwari

Legit.ng ta gano cewa Kakakin hukumar yan sanda na kasa, ACP Jimoh Moshood ya bayar da wata sanarwa a ranar Alhamis, 11 ga watan Mayu inda ya ce wadanda ake zargin wanda suke kungiyoyi guda 5 kuma suna da hannu cikin satar shanu, sayar da makamai da fashi da makami a jihar Zamfara.

KU KARANTA: Wani basaraken musulmi a kudu ya yi umarnin rushe wasu gumaka da jama'a ke bauta

Moshood ya cigaba da cewa abubuwan da aka samu tare da su sun hada da bindigar AK47 kirar kasashen waje guda 2, Ak 47 kirar Najeriya guda 41, Pistol guda 2, bindiga kirar SMG guda 3, Kral magnun guda daya da wasu miyagun makaman.

Ya ce shugaban kungiyar Muhammed Rabiu ya fadawa hukumar gaskiya ne bayan hudu daga cikin yan uwansa sun rasu sakamakon arangamar da sukayi da jami'an tsaro a dajin Bawan Daji da ke karamar hukumar Anka na jihar Zamfara.

"Ya amsa cewa suna suka kashe mutane 46 a yayin da ake jana'izar mutane uku da yan tawagarsa suka kashe a kwanakin baya a kauyen Bawan Daji da ke Zamfara," In ji Moshood.

Sufetan yan sanda, Ibrahim Idris ya ziyarci garin don ganin halin da ake ciki inda kuma ya bayar da umurnin gina wani sansanin yan sanda a garin saboda inganta tsaro a yankin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164