Tsohon Shugaban kasa IBB yayi magana game da rasuwar Isiaka Rabi’u

Tsohon Shugaban kasa IBB yayi magana game da rasuwar Isiaka Rabi’u

Dazu mu ka samu labari cewa Tsohon Shugaban kasar Najeriya a lokacin mulkin Soji Janar Ibrahim Badamasi Babangida yayi magana game da babban Malami Marigayi Sheikh Khalifa Isiaka Rabi’u wanda ya cika a makon nan a Landan.

Tsohon Shugaban kasar yace hankalin sa ya tashi kwarai da ya ji labarin rasuwar babban Shehin ‘Darikar Tijjaniyyar na Najeriya da ma Afrikda da fadin Duniya. Janar Babangida yace tasirin babban Malamin ya ratsa kasar Afrika.

Janar Ibrahim B. Babangida ya bayyana cewa da shi da ma Marigayiyar Mai dakin sa watau Maryam Babangida sun dade su na tare da Iyalan Marigayi Sheikh Isiaka Rabi’u. Babangida yace an yi rashin Bajimin Malami a kaf Najeriya.

KU KARANTA: Mutanen Najeriya sun fara kira Shugaban kasa ya bayyana rashin lafiyar sa

Jaridar Daily Trust ta rahoto IBB yana cewa Malamin mai shekaru 93 ya bar Duniya ne bayan ya cin ma duk burin sa. Tsohon Shugaban na Najeriya yace Shehin Malamin ya taimakawa tattalin arzikin Najeriya musamman ma Yankin Arewa.

A ta’aziyyar da Janar Babangida ya aikawa Jama’an Kano da Mabiya ‘Darikar Tijjaniya a fadin Duniya inda yace Shehin Malamin yayi rayuwar kirki. IBB yace Marigayin mai son zaman lafiya ne da kuma bautar Allah inda ya roka masa rahama.

Yau dai ake sa rai za ayi wa Shehin Malamin sallah a masallacin sa da ke Gorom Dutse a cikin Garin Kano bayan Sallar Juma’a. Shehin Malamin ya cika ne a Ranar Laraba da yamma a kasar waje.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel