Rana zafi inuwa kuna: Yadda ruwan sama ya sanya yan gudun hijira su 2,500 cikin halin ni-yasu
Rana zafi, inuwa kuna, inji yan Hausa, wannan shi ne kwatankwacin halin da wasu yan gudun hijira suka afka tun bayan saukar wani ruwan sama da iska mai karfi aka sha a jihar Borno, inji rahoton jaridar Punch.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito ruwan saman dauke da iska mai karfi sun lalata ma yan gudun hijirar lissafi, inda suka tarwatsa musu dakunan leda da aka yi musu, tare da wancakalar dukkanin kayayyakinsu, wanda hakan ya sabunta halin ni-yasun da mutanen suke ciki.
KU KARANTA: Dubun wasu masu Luwadi a jihar Sakkwato ta cika, sun fuskanci hukuncin Kotu
Ofishin kula da yan gudun hijira na majalisar dinkin Duniya ce ta bayyana wannan lamari da ya faru a ranar Laraba, 9 ga watan Mayu, inda ta daura hotunan barnar da iskar ta yi a shafinta na kafar sadarwar zamani, Twitter.
Ofishin ta bayyana cewar iskar ta yi barna a Kwalejin koyon harshen larabci dake Ngala a jihar Borno, sa’annan ta lalata dakuna 450 na yan gudun hijira, sanadin daya sabbaba ma yan gudun hijira su 2,500 rasa dakuna, inda suka garzaya kauyuka don rabewa.
Sai dai labari mai dadin shi ne alkawarin da ofishin kula da yan gudun hijirar ta yin a cewa za ta fara sake gina dakunan yan gudun hijirar nan bada dadewa ba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng